Shugaban Kasa Zai Ziyarci Kasar Gambiya Yau Laraba

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai tafi Gambia don halartar bikin rantsar da Shugaba Adama Barrow a karo na biyu ranar yau Laraba.

Buhari ne zai kasance baƙo na musamman yayin taron, a cewar wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasa a ranar Talata.

“Bisa gayyatar mai masaukinsa, Shugaba Buhari zai zama baƙo na musamman a bukukuwan da sauran shugabanni a Afirka za su halarta,” in ji sanarwar.

Daga cikin waɗanda za su yi wa Buhari rakiya akwai Ministan Harkokin Waje Geoffrey Onyeama, da Mai Ba da Shawara kan Harkokin Tsaro Babagana Monguno, da Shugaban Hukumar Bayanan Sirri Ahmed Rufai.

Ana sa ran shugaban zai koma Najeriya bayan kammala bikin rantsuwar.

Labarai Makamanta