Shugaban Kasa Ya Taya Sarkin Musulmi Murnar Shekaru 15 A Mulki

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya taya Mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III murnar cika shekara 15 kan gadon sarauta.

Shugaban ƙasa Buhari a cikin sanarwar da mai bashi shawara kan harkokin yaɗa labarai Malam Garba Shehu ya fitar ya bayyana Sarkin a matsayin “mai gina zaman lafiya da jajircewa ga aikinsa, kuma shugaban da ya sadaukar da rayuwarsa wajen kyautata rayuwar al’umma.”

Buhari ya yi wa Sarkin Musulmi fatan samun wasu shekaru masu yawa kan matsayinsa tare da ci gaba da aikin tabbatar da zaman lafiya tsakanin addinai da ƙabilu a sassan Najeriya.

Labarai Makamanta