Shugaban EFCC Ya Buƙaci Ma’aikatan Banki Su Bayyana Kadarorin Su

Hukumar yaƙi da al-mundahana ta ƙasa EFCC ta umarci ma’aikatan banki da su bayyana kadarorinsu da suka mallaka ta kuma bada wa’adi zuwa ranar 1 ga watan Yunin shekarar 2021.

Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar EFCC ne ya bayyana hakan a ranar Talata, yayin da yake zantawa da manema labarai bayan ganawarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ya ce sun tattauna kan kokarin da hukumar ke yi na kawar da laifukan kudi a kasar. Bawa ya bayyana cewa an dauki matakin ne don duba rawar da bankuna ke takawa wajen rike kudaden da suka samu ba bisa ka’ida ba.

“Bari kawai in bayyana wannan, mun fahimci cewa a karshen duk wani laifin kudi shine mai laifi ya samu damar samun kudaden da shi ko ita ta samu ba bisa ka’ida ba kuma muna cikin damuwa game da matsayin cibiyoyin kudi,” in ji shi .

“Kuma mun tattauna, amma muna fatan duk cibiyoyin hada-hadar kudi, musamman ma ma’aikatan banki, za su bayyana kadarorinsu kamar yadda doka ta tanada, kamar yadda Dokar Bayyana Kadarorin Ma’aikatan Banki ta tanada.

“Kuma cewa EFCC, idan 1 ga Yuni 2021 tazo, za ta bukaci wadannan takardun bayyana kadara, wadanda bankunan suka cika domin tabbatar da sharadin da muka gindaya na 1 ga Yuni hakika ma’aikatan banki sun bi shi.”

Shugaban na EFCC ya koka kan yadda hukumar ta damke kimanin masu aikata laifuka ta yanar gizo kimanin 300 a fadin kasar tsakanin watan Fabrairu da Maris.

“A matsayina na matashi, ina kira ga dukkan matasa ‘yan Nijeriya da su guji wadannan ayyukan ta’addanci na yanar gizo. “Yana jawo munanan suna ga kasarmu, yana batawa kasarmu suna, haka kuma yana kokarin salwantar da jarin kasashen waje da muke bukata,” inji Bawa.

“Kuma ina kira ga dukkan iyaye, masu kulawa, da kuma ba shakka, dattawa a cikin al’umma, da su jawo hankalin wadannan matasa don su guji wadannan laifuka.”

Labarai Makamanta