Shugaban Amurka Ya Sha Alwashin Kare Hakkin Musulmi

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce zai ci gaba da kare haƙƙin musulmi a faɗin duniya.

Shugaban ya faɗi haka ne cikin wata sanarwa mai ƙunshe da saƙon fatan alheri ga al’ummar musulmi yayin da suka soma azumin watan Ramadan a ranar Talata.

Shugaban ya ce yana alfahari da ya ɗage haramta wa wasu ƙasashen musulmi shiga Amurka.

“Zan ci gaba da tsayawa kan kare haƙƙin ɗan adam a ko ina, har da ƴan ƙabilar Uyghur a China da rohingya a Burma da kuma dukkanin musulmi a faɗin duniya.

Ya kuma ce dole a kawo ƙarshen barazana da ƙyama da ake nuna wa musulmi a Amurka, a cewarsa: “babu wani a Amurka da zai kasance cikin fargaba don bayyana addininsa.”

A nasa ɓangaren sakataren harakokin wajen Amurka Antonu J. Blinken bayan ya yi wa musulmi murnar Ramadan ya kuma ce Amurka za ta ci gaba da inganta hulɗa da ƙasashen musulmi.

Labarai Makamanta