Shi’a Ta Wallafa Littafin Arangamarsu Da Soji A Zariya

Kungiyar yan Shi’a ta Islamic Movement in Nigeria (IMN), ta bukaci a yi wa mambobinta sama da dubu daya da ta yi zargin an hallaka a 2015 adalci.

Kungiyar ta sake neman wannan bukata ce a wurin bikin kaddamar da wani littafi na musamman da ‘yan Shi’a din suka wallafa a kan abubuwan da suka faru a rikicin sojojin Nijeriya da mambobin mazhabarsu a Zaria jihar Kaduna shekaru shida da suka wuce.

Jaridar Daily Trust ta ce Farfesa Isa Hassan Mshalgaru da ya yi bitar littafin mai suna ‘December 2015 Massacre of Shiites in Nigeria; Survivors Accounts’, y ace amfani da kalmar kisan kiyashi ya yi daidai da abin da aka yi wa mabiya kungiyar IMN a Zaria.

Shima da yake jawabi a wajen kaddamarwar, Babban Sakataren kungiyar Yaki da Cin Hanci da Rashawa, Dr. Ebenezer Oyetokun, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta saki shugaban kungiyar wanda yake tsare tun 2015.

Labarai Makamanta