Shekau Ya Kashe Kanshi Ne Da Kanshi – Salkida

Kwararren mai bada bayanai akan Boko Haram Ahmad Salkida ya tabbatar da mutuwar Abubakar Shekau shugaban kungiyar Boko Haram.

Salkida ya bayyana a shafinsa na Twitter cewar anyi arangama tsakanin Shekau da kuma kungiyar ISWAP, inda ba tare da wani bata lokaci ba Shekau din yayi saranda, ya mika wuya.

Sai dai kungiyar ta ISWAP ta nemi Shekau da yayi mata mubayi’a ya mika jagoranci gareta, inda Shekau din yaki amincewa, kuma ya tarwatsa kansa da Bom. A cewar Ahmed Salkida.

Labarai Makamanta