Shari’ar Musulunci Ta Shafi Musulmi Ne Kawai – Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmai, Alhaji Muhammad Abubakar ya tabbatar wa masu yi wa ƙasa hidima a Sokoto cewa ba za a yi amfani da dokokin Shari’ar Musulunci ga waɗanda ba Musulmai ba.

An ruwaito cewa Sultan Sa’ad ya bayyana hakan ne a ranar ki Alhamis a fadarsa, a lokacin da masu kula da harkokin ƴan bautar kasa karkashin jagorancin shugabansu suka kai masa ziyarar ban girma.

Ya kuma tabbatar musu cewa za su samu tsaro duk da cewa akwai kalubale na tsaro a kasar baki daya.

Abubakar ya kara cewa za a kyale su su gudanar da addinansu.

Ya bayyana cewa ba za a dora wa wadanda ba Musulmi ba hukuncin Shari’ar Musulunci, kuma ya jaddada cewa babu wanda za a tursasa wa shiga Musulunci ba da son ransa ba.

Labarai Makamanta