Shari’ar Karbar Haraji: Gwamnatin Tarayya Ta Nemi Sulhu Da Gwamnoni

Rahotannin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa mafi alheri shine a sasanta tsakanin jihohi da gwamnatin tarayya wajen kotu, kan batun shari’ar wanda ke da haƙƙin karɓar Harajin Jiki Magayi, wato ‘VAT’, wadda ake gwabzawa a kotu.

Idan ba a manta ba, Babbar Kotun Tarayya ta Jihar Ribas da ke Fatakwal ce ta fara bai wa Jihar Ribas iznin cewa ita ke da ikon karɓar Harajin ‘VAT’ a Ribas, ba Gwamnatin Tarayya ba.

Tun daga lokacin kuwa Gwamna Wike ya hana Gwamnatin Tarayya karɓa a jihar sa. Kuma ya kafa sabuwar doka.

Ganin haka, ita ma gwamnatin Jihar Legas ta bi sahun Ribas ta fito da dokar da Majalisar Jihar ta amince da ita cewa ita za ta riƙa karɓar ‘VAT’ a Legas ba tarayya ba.

Su ma Ƙungiyar Gwamnonin Kudu kaf sun goyi bayan Legas da Ribas, cewa jihohi ke da ikon karɓar VAT ba tarayya ba.

Cukumurɗar dai ta samo asali ne ganin yadda ake kwasar kuɗaɗen VAT da gwamnatin tarayya ke karɓa a jihohin da aka fi tara kuɗaɗen shiga, ana gabza wa wasu jihohin Arewa, waɗanda ba su iya tara harajin komai a jihohin su.

A ranar 10 Ga Satumba, Manyan Alƙalan Kotun Ɗaukaka Ƙara su uku, a ƙarƙashin Haruna Tsammani suka umarci ɓangarorin jihar Legas da Ribas da kuma Tarayya cewa kowa ya maida takobin sa cikin kube, su jira hukuncin da za su zartas.

Ita kuwa Ministar Harkokin Kuɗaɗe, Zainab Ahmed cewa ta yi mafi alheri shi ne a yi amfani da teburin siyasa a sasanta a wajen kotu.

“Domin idan aka ce a kotu za a yi ta ta ƙare, to za a ɗauki tsawon lokacin ana gwabza shari’a.”

Musabbabin Rikicin ‘VAT’ Tsakanin Gwamnatin Tarayya Da Jihohi:

Yadda Kotun Tarayya ta bai wa Gwamna Wike iznin
karɓar harajin VAT, ba da son ran Gwamnatin Tarayya ba:

Rikici ya tirniƙe tsakanin Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Ribas, bayan da Babbar Kotun Tarayya da ke Fatakwal ta kwace ikon karɓar harajin ‘VAT’ a Jihar Ribas daga hannun Hukumar Tara Haraji ta Kasa (FIRS), ta danƙa wa gwamnatin jihar.

Lamarin wanda ya faru a ranar Alhamis 19 Ga Agusta, 2021, ya sa nan da nan Gwamna Nysom Wike ya rattaba hannu a kan dokar da Jihar Jihar za ta fara karɓar harajin VAT a jihar, kuma ta hana a riƙa bai wa Gwamnatin Tarayya wannan haraji ta hannun FIRS.

Ba a nan dambarwar ta tsaya ba, haka kuma Babbar Kotun Tarayya ɗin ta yanke hukuncin cewa Gwamnatin Jihar Ribas ce ke da ikon karɓar duk wani haraji a jihar, ba Gwamnantin Tarayya ba.

Wanann hukunci dai kenan ya na nufin kowace jiha za ta iya amfani da wannan hukunci ta riƙa karɓar harajin VAT ta na zubawa aljihun ta kenan.

Kuma hukuncin na nufin an hana Gwamnatin Tarayya karɓar kuɗaɗen haraji a jihohi.

FIRS Ta Ɗaukaka Ƙara:

Hukumar Tara Kuɗaɗen Shiga ta Tarayya (FIRS) ta ɗaukaka ƙara dangane da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta Fatakwal ta yanke, inda ta haramta wa hukumar karɓar harajin VAT a jihar Ribas.

Haka nan kuma wata sanarwa da ta fito daga Babban Jami’in Yaɗa Labarai na FIRS, Abdullahi Ahmad, ya yi kira da kada a bai wa Gwamnatin Jihar Ribas Harajin VAT, a riƙa bai wa Gwamnatin Tarayya, ta hannun FIRS kamar yadda aka saba.

Wannan dambarwa ta faru daidai makon da Najeriya ta sha alwashin tara harajin naira tiriliyan 10.1 cikin 2022.

Gwamnatin Tarayya ta ƙudiri aniyar tara naira tiriliyan 10.1 na kuɗaɗen harajin cikin gida a cikin 2022.

Shugaban Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji ta Ƙasa (FIRS), Mohammed Nami ne ya bayyana haka.

Nami ya yi wannan alwashin a ranar Laraba, lokacin da ya bayyana a gaban Kwamitin Harkokin Kuɗaɗe na Majalisar Tarayya, a Abuja.

Ya ce hukumar sa tuni ta tsara wani tsarin da zai tabbatar an tara waɗannan maƙudan kuɗaɗen cikin 2022.

Nami ya ce za a tara kuɗaɗen ne daga kuɗaɗen harajin da Najeriya ke samu baki ɗaya.

Da ya ke na sa jawabi, Shugaban Kwamitin Harkokin Kuɗaɗe a Majalisar Tarayya, James Dake, ya jinjina wa Shugaban Hukumar FIRS ɗin, kuma ya ƙara masa ƙwarin guiwar ganin cewa an samu waɗannan maƙudan kuɗaɗen da hukumar ta sha alwashin ta tara a cikin shekara mai zuwa.

Labarai Makamanta