Sharhin Bayan Labarai..

Asaalamu alaikum barkanmu da asubahin talata, goma sha biyar ga watan Zulkida, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S A.W. Daidai da bakwai ga watan Yuli na shekarar dubu biyu da ashirin.

 1. Kwamitin bincike na fadar shugaban kasa, ya gayyaci mukaddashin shugaban hukukar EFCC Ibrahim Magu don bincikarsa saboda zargin da ake masa na aikata rashawa. Haka nan hukumar DSS ta ce babu gaskiya a labarin da wasu suka kago cewa ta kama Ibrahim Magu.
 2. Ministan Sufurin Jiragen sama ya ce ba takunkumi ba hawa jirgin sama, kuma an hana masu taimaka wa manyan masu rike da mukaman siyasa, ko mukarraban manyan sojoji ko na manyan ‘yan sanda yi wa iyayen gidansu rakiya zuwa hawa jirgin sama.
 3. Za a soma jarabawar WAEC ranar hudu ga watan gobe na Agusta, a kammala biyar ga watan jibi na Satumba.
 4. Gwamnatin Tarayya ta yafewa gidajen rediyo da talabijin kashi sittin cikin dari na bashin da take bin su, tare da ba su wata uku su biya sauran kashi arba’in, in ba su biya cikin watanni ukun ba, to dole su biya duka kashi darin. Haka nan kudin lasisi an rage da kashi talatin. Sai dai gidajen na rediyo da talabijin sun roki a kara musu wa’adin na wata uku ya zama shekara daya.
 5. Sojojij sama sun ce sun lalata wasu gidaje na shugabannin kungiyar Boko Haram da ke jihar Barno.
 6. ‘Yan bindiga sun kai hari yankin Batsari ta jihar Katsina suka kashe mutane da dama.
 7. Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawal ya nanata cewa sun dakatar da shirin nan na daukar matasa dubu daya a kowacce karamar hukuma da ke kasar nan da suka yi sa-in-sa da karamin ministan kwadago Kiyamo a kai, har sai an je an musu cikakken bayani mai gamsarwa tukuna.
 8. An kwaso wasu ‘yan Nijeriya su tamanin da shida daga Turkiyya.
 9. Gwamnan jihar Ondo Akeredolu ya ce ya warke daga kwaronabairos.
 10. Gwamnan jihar Kogi ya jaddada cewa kwaronabairos wata tatsuniya ce da aka kirkireta don wawurar dukiya ba ‘yar kadan ba. Shi ma gwamnan jihar Kuros Ribas ya ce duk dirama ce kawai babu wata kwaronabairos.Amma kungiyar likitoci ta jihar Kuros Ribas ta ce ita ganau ce ba jiyau ba, akwai kwaronabairos a jihar.
 11. Gwamnatin Tarayya ta yi kashedin kyauta ake gwajin kwaronabairos a asibitocin gwamnati, kuma duk wanda ya bukaci a biya kudin gwajin a sanar da ita.
 12. An debo ‘yan Nijeriya su 57 daga Qatar/Katar.
 13. An ci gaba da shari’ar Babachir Lawal.
 14. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da kusan wata uku ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.
 15. Allah Ya yi wa fitaccen dan siyasa kuma tsohon mataimakin shugaba na shiyyar Arewa Maso Yammacin Kasar nan Inuwa Abdulkadir rasuwa.
 16. Jiya da daddare kafin in kwanta bacci akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos su 575 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 123
Abuja 100
Delta 58
Edo 52
Ogun 42
Katsina 24
Bayelsa 23
Ribas 22
Barno 19
Filato 18
Oyo 17
Kwara 15
Oshun 13
Inugu 9
Nasarawa 7
Abiya 6
Kuros Ribas 5
Kaduna 3
Ekiti 1

Jimillar wadanda suka harbu 29,286.
Wadanda suka warke 11,828.
Wadanda suka riga mu gidan gaskiya 654
Wadanda suke jinya 16,804

Mu wayi gari lafiya.

Af! Jiya ce INTERNATIONAL KISSING DAY. Ranar Sumbata ta Duniya.

Za a iya leka rubutun labarun nawa na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta