Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Asabar, ashirin da tara ga watan Safar, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha bakwai ga watan Oktoban shekarar 2020.

  1. Gwamnatin Tarayya ta umarci dukkan jihohin kasar nan su kafa kwamitocin bincike na shari’a a kan wadanda ‘yan sanda suka ci zarafinsu. Tuni gwamnatin jihar Kaduna ta kafa nata kwamitin, shi kuwa gwamnan jihar Legas Sanwo-Olu, tuni ya fallasa sunayen ‘yan sanda hudu da suka harbi matasan da ke zanga-zangar kawo karshen SARS a Legas.
  2. Matasan Arewa na nan suna ci gaba da zanga-zangar lumana a duka jihohin Arewa, ta neman sai gwamnati ta kawo karshen kidinafin, da kai hare-hare, da zubar da jini, da satar dabbobj, da fyade da sauran matsaloli na tsaro da ke addabar Arewa.
  3. An raba naira biliyan dari shida da talatin da tara, da miliyan casa’in 639,90B na watan Satumba, da ke nuna an kusan jin dilin-dilin na watan Oktoba, kodayake yawancin ma’aikatan gwamnatin tarayya, musamman na foliteknik sai shekaranjiya suka ga dilin-dilin na watan Satumba.
  4. Majalisar Dattawa na so ta ji dalilan da suka sa Hukumar Inshorar Lafiya ta Kasa NHIS ta ajiye wata naira biliyan 122 a wani bankin kasuwanci, har aka samu ribar naira biliyan uku da rabi da ‘yan kai 3.7 B ba tare da izinin gwamatin tarayya ba. Sai dai shugaban hukumar ya ce dokar da ta kafa hukumar ta sakar musu marar juya kudadensu don riba, tunda ba kudaden gwamnati ba ne na hukumar ne.
  5. Gwamnatin Tarayya ta amince za ta ba malaman jami’a da ke yajin aiki naira biliyan arba’in, kudin alawus da suke kira EARNED ALLOWANCE, kuma nan da watan gobe za su ga dilin-dilin na biliyan talatin, allabarshi sauran sa biyo baya a kasafi na gaba. Sai dai shugabanin malaman sun ce ba za su sa hannu a wata yarjejeniya da gwamnatin tarayya ba, har sai sun koma sun nemi izinin sauran malaman da suka tura su tattaunawa da gwamnati tukuna.
  6. Sojojin sama sun ce sun ci gaba da kai hare-hare ta sama, mabuya daban-daban ta kungiyar ISWAP da ke jihar Barno.
  7. Mahukunta kwalejin foliteknik ta Kaduna wato Kaduna Polytechnic, sun umarci dukkan ma’aikatan kwalejin su koma aiki ranar Litinin mai zuwa, jibi ke nan, 19 ga watan nan kamar yadda gwamnatin tarayya ta ba da umarni bayan hutun da aka sha na kwaronabairos.
  8. Da alama mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukunar Kudan ta jihar Kaduna sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru ba su da hanya. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
  9. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata kusan takwas ke nan suna jiran ariyas na sabon albashi.
  10. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 212, da ke nuna a Nijeriya, mutum dubu sittin da daya, da dari da casa’in da hudu ya harbu.

Mu wayi gari lafiya.

Af! A daya daga cikin rubuce-rubucena na makon nan na sa hoton wasu lambobina da na samu na yabo, har na ga wani ya yi tsokacin ya kamata a ce na samu fiye da haka. To wadanda na sa wadanda aka yi su da katakai ne, ga wasu daga cikin wadanda aka ba ni a kwalaye ko takardu kamar haka:

AWARDS

A. MERIT AWARD BY NATIONAL TRANQUILITY MOVEMENT. 1999.

B. MERIT AWARD BY KADUNA STATE MEDIA CORPORATION. 2003.

C. AWARD BY P.T.A. CHAIRMAN KADUNA POLYTECHNIC DEMONSTRATION SECONDARY SCHOOL. 2006.

D. EXCELLENCE AWARD BY P.T.A. KADUNA POLYTECHNIC DEMONSTRATION SECONDARY SCHOOL. 2006.

E. PERFORMANCE AWARD BY KADUNA POLYTECHNIC MANAGEMENT. 2006.

F. LONG SERVICE AWARD BY KADUNA POLYTECHNIC MANAGEMENT. 2007.

G. MERIT AWARD BY KADUNA POLYTECHNIC DEM.SEC.SCH.OLD BOYS ASSOCIATION. 2007.

H. Award of Excellence by Kaduna Polytechnic Demonstration Secondary School Alumni, 21st January, 2017.

I. Certificate of Merit by Kamtos International Schools Kaduna. 2018.

J. Award by Kungiyar Masu Sauraren Shirin Migida Barka Da Rana., January 2018.

K. Certificate of Honorary Membership by Youth Education And Leadership Initiative In Collaboration with the World Leaders Forum, Yeshua, International School of Theology, the Camadan Health Sciences Institute, International Peace Committee for Law, Justice & Human Rights, Friends of the African Union & International Anti-Corruption Bureau.

L. Certificate of Merit by Association of Students of Languages, Department of languages, Kaduna Polytechnic Chapter, 2019.

M. Award of Honour by Rigasa Community, Kaduna. Jan, 2020.

N. Award of Excellent, by Shirin Mu Shakata DITV/Alheri Radio, 2019.

O. Commendation Letter by Management, Staff and Students of Kaduna Polytechnic for the success and achievements recorded as Manager Programmes, Kaduna Polytechnic Spider F.M. Radio, Sept, 2020.

P. Commendation Letter by Radio Nigeria Kaduna. 2018.

Q. Commendation Letter by Kaduna Media Academy, 2018.

Da sauransu.

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a:

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply