Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Laraba, goma sha takwas ga waran Rabi’ul Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da hudu ga watan Nuwamba, na shekarar 2020.

  1. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 137 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 60
Abiya 21
Abuja 18
Ribas 13
Kaduna 5
Oyo 4
Edo 3
Delta 2
Imo 2
Kanno 2
Ogun 2
Bauci 1
Gwambe 1
Nasarawa 1
Neja 1
Oshun 1

Jimillar da suka harbu 63,173
Jimillar da suka warke 59,634
Jimillar da ke jinya 2,388
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1, 151

  1. Jiya na ga Nuhu Yunusa Tankarau na gidan rediyon ABU Samaru FM, ya yi rubutu a dandalinsa na fesbuk kamar haka:

Yanbindiga sunkawo mana hari jiya a yankinmu Na Dutsen Abba,Dake yankin karamar hukumar Zaria,inda suka kwashe mana daruruwan shanu,agaruruwan Tankarau Da kafin Mardanni,kuma sunkashe mana mutum days alokacin harin,daga cikin shanun akwai guda hamsin wadanda mallakinmune nida yayana,Dafatan Allah ya mayarmana da alkhairi Ameen,

  1. Gwamnatin Tarayya ta ce ita fa a nata bangaren ta biya wa malaman jami’a bukatunsu, saboda haka ba ta ga dalilin da ya sa malaman ke ci gaba da yajin aiki ba.
  2. A yanzun kidinafas sun bullo da wata sabuwar tsirfa, ta zuwa asibiti ko masallatai su tarkata jama’a su yi awon gaba da su, sai an biya kudin fansa, kamar yadda suka yi a jihar Nasarawa.
  3. Ma’aikatan man fetur da na gas, PENGASSANG da NUPENG, sun ba da zuwa Litinin, ko gwamnati ta yi wani abu a kan albashinsu da suke bi na wata da watanni da kuma batun IPPIS, ko su janye jiki daga ayyukansu daga litinin din.
  4. Kudaden Gwamnatin Tarayya na kasashen waje, sun kara auki daga Dala Miliyan goma sha shida da kusan rabi, zuwa Dala Miliyan talatin da biyar da rabi da ‘yan kai.
  5. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na Gwamnatin Tarayya, na korafin idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekara mai zuwa, sun cika shekara biyu ke nan suna zaman jiran ariyas na sabon albashi.
  6. Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru ba su da hanya. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Jiya na tallata kadan daga cikin hajar kamfanin Guibi-Hausa Services, sai dai na so in yi tuya in manta da albasa.
Kamfanin na sayar da kalmomi/kalamai na soyayya, wato na tsara budurwa ko saurayi, ko tsara bazawara ko bazawari, har a kai ga aure. Wato kamfanin na sayar da tsararrun kalamai masu ratsa zuciyar masoyi ko masoyiya, da za su taimaka a kai ga nasarar sace zuciya har a kai ga aure. Kana irin sonta din nan tana ta ba ka wahala, ko ba ka san kalaman da za ka yi amfani da su ka shawo kanta ba. Sai ka garzayo kamfaninmu ba tsada.

Yanzun karfe hudu da minti hudu na asubah, ga ladanai can suna rige-rigen kiran assalatu.

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply