Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalama alaikum barkanmu da asubahin alhamis ashirin da hudu ga watan Zulkida shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha shida ga watan Yuli na shekarar dubu biyu da ashirin.

  1. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kaduwarsa a kan mutuwar soja mayakiyar jirgin sama ta farko a kasar nan Temitope Arotile ‘yar asalin jihar Kogi da tsautsayi wasu wadanda suka taba yin karatu tare suka yi kokarin irin sun ganta a kafa bari a juyo a dauketa, wajen juyowar suka bugeta a nan Kaduna, ta riga mu gidan gaskiya, mai shekara ashirin da biyar a duniya.
  2. Kidinafas da suka jidi mutum wajen ashirin bayan sun kashe na kashewa a unguwar KK da ke cikin garin Kaduna sun kira waya suna bukatar naira miliyan dari tara kudin fansa.
  3. Lauyan Magu Tosin ya ce an saki Magu da ya kusan kwana goma a tsare ana masa tambayoyi.
  4. An bude duka tashoshin jiragen sama na kasar nan don ci gaba da zirga – zirga.
  5. Kungiyar malaman kwalejojin ilimi ta ba gwamnatin tarayya wa’adin mako biyu ko ta waiwaye su, ko su yi yaji.
  6. Kotu ta daure tsohon shugaban hukumar NIMASA mai kula da kiyaye hadurra da makamatansu a tashoshin ruwa Agaba daurin shekara bakwai saboda wata damfara.
  7. An ci gaba da shari’ar Hamisu Wadume da sauran mutane shida a Abuja har aka gabatar da bindiga kirar AK47 guda shida shaida.
  8. An ce zuwa shekarar dubu biyu da dari yawan ‘yan Nijeriya zai zarce na ‘yan Caina a duniya.
  9. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya na ci gaba da korafin shekara daya da wata uku ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.
  10. Jiya kafin in kwanta bacci akwai sabbin harbuwa da kwarona 643 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 230
Oyo 69
Abuja 51
Edo 43
Oshun 35
Ribas 30
Ebonyi 30
Kaduna 28
Ogun 27
Ondo 23
Filato 20
Binuwai 17
Inugu 16
Imo 10
Delta 6
Kano 4
Nasarawa 2
Kabbi 1
Ekiti 1

*Kaduna 28, Kano 4 !

Jimillar wadanda suka harbu 34,259
Jimillar wadanda suka warke 13,999
Wadanda suka riga mu gidan gaskiya 760
Wadanda ke jinya 19,500

Kaduna na da jimillar 1,063
Kano na da jimillar 1,318

Mu wayi gari lafiya.

Af! Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai tsaro fa ba shi da lafiya a jiharka kuma hakkinka ne.

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta