Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin lahadi, goma ga watan Muharram, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin anabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da talatin ga watan Agusta na shekarar dubu biyu da ashirin.

  1. Yawancin ma’aikatan kwalejojin filiteknik da ke ci gaba da ganin dilin-dilin na wannan watan na ta korafin an musu kwange a albashin watau albashin ya zo amma an yanke wani abu daga ciki an masa gibi wasu ma wawulo.
  2. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata shida ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi har yau shiru.
  3. Talakan Nijeriya na ci gaba da korafi a kan tsadar rayuwa. Kama daga kayan abinci zuwa kayan miya, da sauran kayan abin masarufi duk sai kara tsada suke yi a kullum garin Allah Ya waye.
  4. Masu ababen hawa na ci gaba da korafin masu gidajen mai na tauye musu mudu ko lita. Idan ka je sayen mai na naira dubu daya a misali, tabbas mitar ko famfon zai nuna an zuba maka man naira dubu daya, amma a zahiri bai wuce man naira dari tara aka dura maka ba. Suka ce ga man kamar iska, ana zuba maka kana matsawa nan zuwa can sai ka ga ya yi batar dabo daga tankinka.
  5. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da korafin shekara da shekaru ba su da hanya, wata da watanni ba su da wutar lantarki, ga tsadar taki, ga gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan suka zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi, ga wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
  6. Talaka na korafin shinkafa da masara na kokarin gagararsa duk da a nan cikin gida ake noma su. Shi kuwa manomin da ya noma shinkafa da masara bana, yana ta darawa har kunne.
  7. APC na ci gaba da zargin PDP da gwamna Obaseki na ta ruwan kudi don murde zaben gwamna na jihar Edo da za a yi. Zargin da PDP ta musanta.
  8. Iyaye da yara a jihar Legas na ci gaba da korafin yara na gida ba zuwa makaranta saboda kwaronabairos. Sai dai gwamnan jihar ya musu albishir cewa za a bude jami’o’i da sauran manyan makarantu da ke jihar ranar goma sha hudu ga watan gobe na Satumba don ci gaba da karatu, su kuma ‘yan firamare da sakandare za su koma ranar ashirin da daya ga watan na gobe.
  9. Duniya na ci gaba da korafi da nuna tsoronta a kan gwajin makaman kare dangi a daidai lokacin da jiya ta kasance ranar kyamatar gwajin irin wadanan makamai a duniya bakidaya.
  10. ‘Yan Nijeriya na ci gaba da korafi a kan yadda cutar kwaronabairos ta jefa su cikin halin kunci na rayuwa, a daidai lokacin da sabbin wadanda suka harbu a jiya, su 250 ne a jihohi da alkaluma kamar haka:

Filato 69
Abuja 41
Legas 21
Delta 14
Kaduna 14
Bayelsa 13
Ekiti 11
Bauci 9
Ogun 8
Edo 7
Oyo 7
Ribas 6
Adamawa 4
Oshun 4
Nasarawa 3
Ebonyi 2
Kwara 2
Gwambe 1
Imo 1

Jimillar da suka harbu 53 727
Jimillar da suka warke 41,314
Jimillar da ke jinya 11,402
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,011

Mu wayi gari lafiya.

Af! Ina nan ina ci gaba da korafin yau labarun ba yawa saboda ana hutu na karshen mako da akan yi kamfar labarun.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta