Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin alhamis, bakwai ga watan Muharram, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da bakwai ga watan Agusta na shekarar dubu biyu da ashirin.

  1. Yau ashirin da bakwai ga wata, ma’aikata sun fara korafin hantsi ya soma duban bakin ludayi, wato lokacin jin dilin-dilin ya yi.
  2. Farashin kayan abinci na ci gaba da tashin gwauron zabi. Garin masara kwatan buhu da na saba saya naira dubu biyu, ya kai naira dubu uku, ya kai naira dubu hudu, a karshen watan jiya da muka ji dilin-dilin na sayo shi naira dubu bjyar. To jiya na sayo shi naira dubu biyar da dari bakwai da hamsin. Na san zuwa karshen watan nan zai kai naira dubu shida. Rabin buhu ya zama naira dubu goma sha biyu. Buhu naira dubu ashirin da hudu. Buhun da nake saya a naira dubu takwas a da.
  3. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata shida ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi, har yau shiru.
  4. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci taron Majalisar Zartaswa karo na goma sha uku da ake yi ta intanet. Inda a batun binciken hukumar raya yankin Neja Delta NDDC, aka mata karin naira miliyan dari bakwai da ashirin da hudu.
  5. Babban Bankin Nijeriya CBN ya ce ya kashe naira biliyan saba’in da biyar wajen buga kudin Nijeriya a shekarar dubu biyu da goma sha tara.
  6. Femi Kayode ya ba da hakurin zagin da ya yi wa wani dan jarida wakilin jaridar Daily Trust, da ya cewa STUPID don ya tambaye shi wa ke daukar hidimar zagayawar da yake yi wasu jihohi duba ayyukan da suke yi.
  7. Kwalejin Horas da Kananan Hafsoshin Soja NDA da ke Kaduna, ta ankarar da jama’a su yi hattara da wasu ‘yan damfara da ke bude dandali a soshiyal midiya da sunan kwalejin.
  8. Kungiyar Lauyoyi ta Kasa ta yi babban taron nata karo na sittin, taron da aka yi takaddama a kan gayyatar Malam Nasir El-Rufai, da Obasanjo da Wike.
  9. Majalisar Dinkin Duniya ta martaba ma’aikatan da kungiyar Boko Haram ta kashe lokacin hare-harenta a shekara tara.
  10. Sojoji sun damke mahara dari da sittin da kashe uku a jihar Zamfara.
  11. Kotu ta dakatar da PDP ta jihar Kaduna daga gudanar da babban zabenta na karamar hukuma da na jiha.
  12. Gwamnatin jihar Jigawa ta ba da hutu don zagayowar ranar da aka kirkiro jihar.
  13. Ruwanda ta sa a damko mata wanda take zargin shi ya kitsa fadan-kare-dangi da aka yi a kasar, da aka ji duriyarsa yana kasar Faransa.
  14. Kungiyar kasashen da Faransa ta mulka ta duniya International Franchophone Organisation, ta fatattaki kasar Mali daga cikinta saboda juyin milkin da sojoji suka yi a kasar.
  15. Malaman jami’a na Nijeriya na nan sun ce za su ci gaba da yajin aiki, kodayake na ga wani labari da ke cewa suna kira ga gwamnati ta bude manyan makarantun kasar nan.
  16. A yanzun a duniya, wadanda suka harbu da kwaronabairos sun kai miliyan ashirin da hudu babu ‘yan kadan.
  17. A Nijeriya akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 221 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Filato 60
Abuja 33
Kaduna 26
Ribas 18
Legas 17
Inugu 9
Kwara 9
Ondo 9
Nasarawa 6
Gwambe 5
Anambara 5
Delta 4
Abiya 4
Imo 3
Edo 2
Ogun 2
Oyo 2
Oshun 2
Bauci 1
Kano 1

Jimillar da suka harbu 53,021
Jimillar da suka warke 40,281
Jimillar da ke jinya 11,730
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,010

Mu wayi gari lafiya.

Af! Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da kasancewa a killace, shekara da shekaru ba hanya, wata da watanni ba wuta, damina ta yi nisa taki na tsada. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Shugaban karamar hukumar Kudan na yanzu, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan suka zabe shi zai gyara musu gadar. Sun zabe shi ga wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2686706854935042&id=2356865571252507

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta