Assalamu alaikum barkanmu da asubahin alhamis, ashirin da uku ga watan Zulhijja, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha uku ga watan Agusta, na shekarar dubu biyu da ashirin.
- Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna ci gaba da zama a killace, ba shiga ba fita, sakamakon ballewar gadar da sukan samu su haura, da shugaban karamar hukumar Kudan, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Ga wa’adinsa na shirin karewa ya kasa gyara musu.
- Wasu malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya na ci gaba da korafin wasunsu suna bin albashi na wata daya, wasu wata biyu, wasu wata uku, wasu wata hudu wasu biyar. Haka nan ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwanatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata biyar suna dakon ariyas na sabon albashi, har yau shiru.
- Yanzun karfe hudu da minti ashirin da uku na asubah. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos su 453 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Legas 113
Abuja 72
Filato 59
Inugu 55
Kaduna 38
Ondo 32
Oshun 26
Ebonyi 20
Ogun 9
Delta 8
Barno 7
Akwa Ibom 6
Oyo 5
Bauci 1
Kano 1
Ekiti 1
Jimillar da suka harbu 47,743
Jimillar da suka warke 33,943
Jimillar da ke jinya 12,844
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 956
- Ministan harkokin wajen kasar nan Geofrey ya warke daga kwaronabairos.
- Hukumomin sojan sama sun kara dagewa wajen kai wa inda ‘yan Boko Haram suke hari, da kashe da dama daga cikinsu.
- Hukumomin soja sun ce suna nan suna bincike a kan zargin da gwamna Zulum ya yi cewa sojoji ba sa son rigimar Boko Haram ta kare ne, saboda suna can a Baga suna ta nome gonakin jama’a da sana’ar kamun kifi.
- Hukumomin soja sun hukunta wani soja kofur, daurin shekara arba’in da biyar, wata ruwayar ta ce daurin shekarar hamsin da biyar ne saboda laifuka daban-daban da ya aikata wa farar hula da sauransu.
- Gwamnatin tarayya ta amince da wata naira biliyan takwas da kusan rabi don sayo kayan aikin gwajin gano masu kwaronabairos.
- Gwamnan jihar Binuwai Ortom, ya kawo shawarar a kyale kowanne talaka ya mallaki bindiga kirar AK47 don ya iya kare kansa daga masu yawan kai masa farmaki.
- Hukumar kwastam ta kwace katan dubu uku da dari bakwai da casa’in na magunguna jabu a jihar Kaduna, ta mika wa hukumar NAFDAC ta kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa.
- Otaru na Auchi ya nada dan takaran gwamnan jihar Edo na jam’iyyar APC fasto Osagie sarautar Itsemakhowa na Auchi.
- Hukumar tsaro ta DSS ta gayyaci tsohon mataimakin shugaban babban bankin Nijeriya Obadiya Mailafiya a kan wani tsokaci da ya yi a kan kungiyar Boko Haram, daga baya ta sallame shi, sai dai gwamnonin Arewa sun kawo shawarar a binciki maganar ta Mailafiya don biri ya so ya yi kama da mutum.
- Manyan ma’aikatan manfetur sun soma yajin aiki na gargadi na kwana uku.
- An kwaso wasu ‘yan Nijeriya su casa’in da hudu daga Labanan zuwa Legas.
- Gwamna Masari ya hana kungiyoyin nan da ba na gwamnati ba da aka fi sani da NGOs zuwa sansanonin ‘yan gudun hijira da aka fi sani da IDP Camps da ke jihar Katsina.
- ‘Yan bindiga sun ci gaba da kai hari kauyukan jihar Katsina, su kashe na kashewa, su sace na sacewa, su jidi dabbobi son ransu su yi gaba
- Hukumar Zabe ta kasa ta sa karshen watan Oktoba don gudanar da zabukan cike gurbi a wasu jihohi, na ‘yan majalisa.
- Shugaban kasa ya nada Adamu Adaji a matsayin babban shugaban hukumar kula da al’amuran kan iyaka.
- Hukumar kula da raba daidai ta kasa ta ce za ta sanya ido don tabbatar da ana raba daidai wajen daukar ma’aikata aiki a ma’aikatun tarayya da mukamai.
- Hukumar tace da tsabtace bidiyo da fina-finai ta kasa na shirin bullo da rajistar dole, ta abubuwan da bidiyo da fina-finai suke kunsa.
Mu wayi gari lafiya.
Af! Oh! Karya dai fure take yi ba ta ‘ya’ya. Da ma na ce tusa ba ta hura wuta. Kuma ramin karya kurarre ne. Allah Ka raba mu da sharrin mutum, mutumin ma da kuke tare a kowanne lokaci yake cin gajiyarka da moriyarka, yana wage maka hakora, amma ta ciki na ciki. Jama’a a ce AMIN.
Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.
You must log in to post a comment.