Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin laraba, ashirin da biyu ga watan Zulhijja, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha biyu ga watan Agusta na shekarar dubu biyu da ashirin.

 1. Shugaban Kasa Muhamadu Buhari ya sake neman ahuwan ‘yan Nijeriya a kan matsalar tsaro, tare da ba su tabbacin nan gaba kadan komai zai wuce. Ya ce a yanzun haka Nijeriya za ta sayo kayan yakar ‘yan bindiga daga Jordan da Amurka da Caina.
 2. Jiya shugaban kasa Muhamadu Buhari ya sake yin wani taro da manyan hafsoshin tsaro, da wasu gwamnoni duk a kan gano bakin zaren magance matsalar tsaro.
 3. Kungiyar Bishop-Bishop na Arewa ta yi kiran a kawo karshen kashe-kashe a kudancin jihar Kaduna, da biyansu diyya, da yi wa bangaren tsaron kasar nan garambawul.
 4. Wata kididdiga da na gani jiya a shirin JOURNALISTS’ HANGOUT na gidan talabijin na TCV NEWS na cewa a watanni bakwai da suka gabata kadai, a Arewa ‘yan bindiga sun kashe farar hula dari biyu da ashirin da takwas, da sojoji tamanin da biyu, da ‘yan sanda bakwai.
 5. Tsohon shugaban kasa Jonathan ya kuma komawa kasar Mali don ganin yadda za a aiwatar da tsarin kungiyar ECOWAS na zaman lafiya a can.
 6. Wasu ‘yan bindiga sun kai hari Kona da ke jihar Taraba, suka kashe mutum daya, kasa da sa’o’i ashirin da hudu bayan kashe wani mai suna Shamaki mai wata makaranta.
 7. Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Fafilani da ke mazabar Dutsen Abba a karamar hukumar Zariya ta jihar Kaduna, suka yi awon gaba da dabbobi sun haura dari uku.
 8. Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum a kalla goma sha daya a jihar Binuwai a kan wata rigima ta sarautar gargajiya.
 9. Gwamna Zulum ya bukaci sojoji su ceto garuruwan da ke bakin tafkin Cadi da dajin Sambisa daga hannun kungiyar Boko Haram.
 10. Sojoji sun damke wasu mutane takwas da suke zargin su ke kashe-kashe a kudancin jihar Kaduna.
 11. Hukumar shirya jarabawa ta kasa NECO ta fitar da nata jadawalin jarabawar.
 12. Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i da sauran manyan makatantu JAMB ta soma adimishan.
 13. Hukumar EFCC ta kama wasu ‘yan damfara ta intanet su talatin da uku.
 14. Amurka ta cika alkawarin da Donald Trump ya yi wa shagaban kasa Buhari na bai wa Nijeriya na’urar taimaka wa yin numfashi ga majinyantan kwarona guda dari biyu.
 15. Wata makaranta a Masko ta kasar Rasha ta yi nasarar gano maganin kwaronabairos kuma tuni aka amince a yi amfani da shi, sai dai Amurka da ke da kusan mutum miliyan biyar, kwatan wadanda suka harbu da cutar a duniya na dari-dari da maganin.
 16. Majalisar Dokoki ta jihar Kaduna ta dakatar da tsohon mataimakin shugaban majalisar.
 17. ‘Yan majalisar dokoki ta jihar Edo bangaren su bakwai da ke tare da gwamna Obaseki sun yi nasu zaman majalisar jiya.
 18. Wasu malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin rabonsu da albashi, wasunsu wata biyar, wasu hudu, wasu uku, wasu biyu wasu wata daya. Kamar yadda ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, ke ci gaba da korafin shekara daya da kusan wata biyar ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.
 19. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da kasancewa a killace ba shiga ba fita, sakamakon ballewar da gadar da sukan samu su haura ta yi, da shugaban karamar hukumar Kudan, Jaja ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe idan sun zabe shi zai gyara. Ga wa’adinsa na shirin karewa har yau bai gyara musu ba.
 20. Yanzun karfe hudu da minti ashirin da hudu na asubah, akwai sabbin harbuwa da kwarona su 423 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 117
Abuja 40
Ondo 35
Ribas 28
Oshun 24
Binuwai 21
Abiya 19
Ogun 19
Ebonyi 18
Delta 17
Kwara 17
Kaduna 15
Anambara 14
Ekiti 11
Kano 9
Imo 6
Gwambe 4
Oyo 3
Taraba 3
Bauci 1
Edo 1
Nasarawa 1

Jimillar da suka harbu 47,290
Jimillar da suka warke 33,609
Jimillar da ke jinya 12,725
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 956

Mu wayi gari lafiya.

Af! Jihar Kogi dai ba ruwanta da kwaronabairos. Gwamnansu Yahya Bello ya ‘yanta su. Ba harbuwa, ba jinya, ba warkewa, ba mutuwa, ba hana Sallah, ba rufe kasuwa, ba tilasta sa takunkumi, ba batun tazara, ba kotun – tafi – da – gidanka.

Na yi nan.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta