Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalama alaikum barkanmu da asubahin talata, ashirin da daya ga watan Zulhijja, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha daya ga watan Agusta, shekarar dubu biyu da ashirin.

 1. Gwamnonin jihohin Arewa Maso Gabashin kasar nan sun kai wa shugaban kasa Muhamadu Buhari ziyara, tare da rokonsa a iganta tsaro a yankin, da ci gaba da neman manfetur a yankin, da raya kogunan yankin domin ci gaban jama’ar yankin.
 2. Wasu ‘yan bindiga sun kuma shiga kauyukan jihar Katsina, wuraren Kurfi, wata ruwayar na cewa sun yi kidinafin wani, wata na cewa wata suka yi kidinafin, wata ruwayar ke cewa sun tafi da mutane da dama.
 3. Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani mai makaranta a jihar Taraba.
 4. Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum takwas a Nijar, har da Faransawa mutum shida.
 5. Jami’an tsaron kasar Nijar sun bindige wasu fataken da ke safarar makamai daga Libiya suna kawo wa ‘yan bindiga da ke Arewa Maso Yammacin kasar nan, hudu sun mutu sakamakon harbin, suka kama daya.
 6. Gwamnatin jihar Bauci ta yi wa masu baburan da ta kwace baburansu gwanjon baburan nasu.
 7. A makon gobe ake sa ran kwamitin shugaban kasa da ya yi wa Magu tambayoyi zai mika wa shugaban kasa rahotonsa.
 8. Kotu a jihar Kano ta yanke wa mutum biyu babba da yaro hukunci. Shi yaron shekara goma a gidan gyara halinka saboda shekarunsa ba su kai a masa hukuncin da ya fi haka ba, babban kuma hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda laifuka na batanci ga Allah da manzonSa.
 9. Kungiyar Agaji ta Musulunci ta Duniya I.I.R.O. a takaice, za ta tallafa wa marayu dari bakwai da saba’in da takwas da ke jihar Sakkwato.
 10. Can na tsinci wata takarda da ke yawo a wasaf, da aka ce daga gwamnatin jihar Kaduna ta fito, tana umartar ma’aikatan jihar da ke samun albashinsu ta bankin FIRST BANK, su hanzarta canza banki. Ina sahihancin takardar? Inda gaske ne ina dalili?
 11. Wasu malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin wasunsu rabonsu da albashi wata biyar, wasu wata hudu, wasu wata biyu, wasu wata daya. Haka nan ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da kusan wata biyar ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi, har yau ba amo ba labari sai wani jadawalin lissafi aka bar su da shi.
 12. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da kasancewa a killace ba shiga ba fita saboda ballewar gadar da sukan samu su haura, da shugaban karamar hukumar Kudan, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu, ga wa’adinsa na shirin karewa har yau bai iya gyara musu ba.
 13. Yanzun karfe hudu daidai na asubah, akwai sabbin harbuwa da kwarona su 290 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 82
Filato 82
Oyo 19
Abuja 18
Edo 16
Kaduna 15
Inugu 9
Ogun 9
Kano 8
Kwara 8
Kuros Ribas 5
Ondo 5
Ribas 5
Ekiti 4
Imo 3
Barno 2

Jimillar da suka harbu 46,867
Jimillar da suka warke 33,346
Jimillar da ke jinya 12,571
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 950

 1. Yawancin makarantu da suke da dalibai da za su rubuta jarabawar fita sun koma jiya.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Can a wani dandalin wasaf na ‘yan Doka da ke yankin karamar hukumar Kudan na ga wani na kokarin nuna kamar ni ba dan yankin Kudan ba ne. Yana korafin na dame su da rubutu. To ni haifaffen kauyen Guibi ne cibiyata na Guibi, iyayena da kakannina na Guibi, har firamaren Guibi na yi, na yi sakandaren Kudan, daga aji daya zuwa biyar (form one to form five) na gama a 1986.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta