Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Juma’atu babbar rana, goma sha bakwai ga watan Zulhijja, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da bakwai ga watan Agusta na shekarar dubu biyu da ashirin.

  1. Gidajen rediyo da talabijin sun yi korafin su fa har yanzun ba su gani a kasa ba, batun da ministan labaru Lai Mohamed ya yi cewa an yafe wani kaso cikin kudaden da gwamnatin tarayya ke bin gidajen rediyo da talajin. Suka yi korafin Lai Mohammed ne idan ya kwankwadi shayi ya kai masa, sai ya tara manema labaru ya dinga fadin abubuwan da suka saba wa gabadaya tsarin kafofin watsa labaru, da kokarin durkusar da gidajen rediyo da talabijin da ke zaman kansu, ta wasu ka’idoji da yake bullo da su, kamar tarar nan da ya kara daga naira dubu dari biyar, zuwa naira miliyan biyar ga duk wanda ya yi kalaman kiyayya ko kin jini a kafofin watsa labaru.
  2. Ta tabbata an kara kudin mai a yanzun ya koma naira dari da hamsin kowacce lita. Dillalan man da ke zaman kansu sun ce hukumar kayyade farashin mai ta kasa ce ta yi karin kudin a daffo-daffon man daga naira dari da talatin da uku da kwabo saba’in da biyu kowacce lita, zuwa naira dari da talatin da takwas da kwabo sittin da biyu kowacce lita.
  3. Gwamnatin Tarayya ta ce babu gaskiya a zargin da daliban Nijeriya da ke karatu a Saudiya suka yi cewa tun goma sha biyar ga watan Mayu na shekarar nan aka ba su hutu, gwamnatin tarayya ta yi watsi da su ba ta kwaso su zuwa gida ba.
  4. Ana nan ana shirin maido da zirga-zirgar jiragen sama na kasashen duniya a tasoshin jiragen sama na Nijeriya.

5 . Gwamnatin tarayya ta dore da matakan kulle da ake ciki na karin makwanni hudu amma da ‘yan sauye-sauye kamar bude makarantu don dalibai masu rubuta jarabawar fita, da karin sa’o’in da manyan ma’aikata ke yi a wuraren ayyukansa da sauransu.

  1. Amurka ta ankarar cewa ‘yan kungiyar Alka’ida na tuttuda zuwa yankin Arewa Maso Yammacin Kasar nan don samun gindin zama.
  2. Ma’aikatan lafiya na jihar Bauci sun soma yajin aiki, shi kuwa gwamnan jihar Ekiti ya yi wa likitoci da ke yajin aiki a jihar barazanar ba aiki ba albashi.
  3. Jiya wasu ‘yan majalisar dokoki ta jihar Edo suka tsige shugaban majalisar da mataimakinsa, sai dai gwamnan jihar Obaseki da jam’iyyarsa ta PDP sun ce tatsuniya ce.
  4. Gwamnatin jihar Oyo ta fitar da naira miliyan kusan sittin don kankamar rundunar tsaro ta Amotekun a jihar.
  5. Gwamatin jihar Binuwai ta gano sunayen malaman bogi su dari bakwai da ashirin da hudu cikin jerin sunayen malaman da ake biya albashi.
  6. Hukumar zabe ta kasa ta soma horas da jami’an tsaro, horaswa ta yini uku a kan zaben da za a yi na jihar Edo. Sai dai hukukar zaben ta ce ba za ta yi wata-wata ba wajen dage zaben jihar idan aka ki zama lafiya.
  7. Shugaban karamar hukumar Zangon Kataf ta jihar Kaduna Elias ya ce jiya da safe wasu da yake zargin fulani ne sun kai hari al’umomi uku da ke yankin, suka kashe mutum a kalla ashirin da biyar, da kona gidaje da dukiyoyi.
  8. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin har yau shekara daya da wata hudu ba su ga ariyas na karin albashi ba.
  9. Mutum kusan miliyan goma sha tara ba dan kadan ya harbu da kwaronabairos a duniya. Sannan mu a Nijeriya a daidai wannan lokaci karfe hudu da wasu mintoci na asubah, da nake wannan rubutu, akwai sabon harbuwa mutum 354 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Abuja 78
Legas 76
Kaduna 23
Ebonyi 19
Oyo 18
Nasarawa 17
Ribas 17
Delta 16
Kwara 19
Akwa Ibom 13
Edo 12
Ogun 12
Filato 11
Kano 9
Bauci 6
Barno 6
Ekiti 6

Jimillar da ya harbu 42,244
Jimillar da ya warke 32,430
Jimillar da yake jinya 8,884
Jimillar da ya riga mu gidan gaskiya 930

A nemi jaridar Leadership Hausa A Yau Juma’a da za ta fito an jima da safe don karanta shafukana da ke dauke da rubutun labarun da na kawo muku daga juma’ar da ta gabata zuwa jiya alhamis.

Mu wayi gari lafiya, mu yi juma’a lafiya.

Af! Na kuwa so in ji wadanda gwamnati ke cewa tana kwaso su daga kasashen ketare zuwa gida Nijeriya na korafin ba kyauta ake kwaso su ba, sai an tatike musu kudadensu ake kwaso su.

Af!! Mutanen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna na can a killace a kauyen ba shiga ba fita sakamakon ballewar gadar da sukan samu su haura, da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzu, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi, zai gyara musu. Ga wa’adinsa na shirin karewa ya kasa gyara musu.

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta