Assalamu alaikum barkanmu da asubahin alhamis, goma sha shida ga watan Zulhijja, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da shida ga watan Agusta na shekarar dubu biyu da ashirin.
- Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya leka fadar shugaban kasa ya zanta da shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan matsalar tsaro.
- Hukumomin soja sun ce babu gaskiya a zargin da Gwamna Zulum ya yi cewa sojoji ne suka kai masa farmaki ba ‘yan kungiyar Boko Haram ba. Hukumomin suka ce da jin karar bindigogin da yanayin harbin, bindiga ce irin ta ‘yan Boko Haram ba ta sojojin Nijeriya ba.
- Jami’an tsaro sun tarwatsa wasu da suka yi zanga-zanga jiya ta neman shugabanci na gari a kasar nan #revolutionnow protest a Abuja da Legas da Oshun.
- Wasu ‘yan Nijeriya na mayar da martanin cewa ba kara kudin tarar kalaman kiyayya daga naira dubu dari biyar zuwa naira miliyan biyar ce matsalar da ta fi ci wa Nijeriya tuwo a kwarya a yanzun ba, illa matsala ta tsaro.
- Sakamakon korar direbobin jiragen sama da kamfanin Air Peace da na Bristow suka yi, direbobin jiragen sama, da injiniyoyin jiragen sama, sun ba gwamnatin tarayya wa’adin mako biyu ta hana ci gaba da korarsu da tilasta dawo da wadanda aka kora, ko a gan su a rana da ita gwamnatin. Kamfanonin na korar ma’aikatansu ne saboda kwarona da ta shafi sabgar shiga jirgi.
- An kwaso karin ‘yan Nijeriya dari uku da shida daga Amurka.
- ‘Yan Nijeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu a kan bayanin da gwamnatin tarayya ta yi cewa ta kashe naira miliyan dari biyar wajen ciyar da ‘yan makaranta a lokacin da ake cikin kulle na kwaronabairos a kasar nan.
- Gwamnatin Tarayya ta sawo wa sojojin saman kasar nan karin jiragen sama na yaki.
- ‘Yan sanda a jihar Katsina sun damke wasu nas-nas guda biyu da ke badakalar jarirai.
- Ana batun za a kara farashin man fetur.
- Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da zaman kulle a kauyen saboda ba gadar shiga da fita, saboda ta lalace, duk da shugaban karamar hukumar ta Kudan ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe cewa idan suka zabe shi zai gyara musu gadar, ga wa’adinsa na shirin karewa gadar ta gagara gyara.
- Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata hudu ke nan suna jiran ariyas na sabon albashi, har yau ba amo ba labari.
- Masu bibiyata da dama sun yi korafin ba su iya ganin rubutuna na jiya ta fesbuk ba. To ni ma ban san dalili ba. Amma tabbas na yi rubutu jiya kuma wasu sun yi tsokaci.
- Yanzun karfe hudu da kusan rabi na asubah, akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos guda 457 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Legas 137
Abuja 76
Filato 40
Ribas 35
Inugu 34
Oyo 25
Abiya 23
Delta 12
Edo 11
Ebonyi 11
Kuros Ribas 10
Kwara 10
Kaduna 9
Anambara 7
Ogun 5
Imo 3
Bauci 3
Oshun 2
Nasarawa 2
Kano 1
Ekiti 1
Jimillar da suka harbu 44,890
Jimillar da suka warke 32,165
Jimillar da ke jinya 11,798
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 927
Mu wayi gari lafiya.
Af a labarun da na bayar shekaranjiya talata, akwai wanda kiristocin kudancin jihar Kaduna suka yi kira ga kiristocin su dage da addu’a da azumi na wata daya don rokon Allah Ya kawo karshen kashe-kashen da ake yi a can. A wadanda suka yi tsokaci a kai har da Alhassan Balarabe Musa da ke cewa :
‘ ‘Yan uwan mu dake kudanci ya kamata su fahimci babu azumin da zai kawo Zama lafiya a kudancin kaduna idan babu ADALCI.
Anyi rigin gimu da yawa a kudancin kaduna Amman me ya chanza a kudancin kaduna. Kullum jama’arsu na cikin talauci, da kuncin rayuwa. sun Sami Ministoci, MANYAN sakatarorin gwabnatin tarayya MANYAN sojojin da wasu sunyi gwabnan soja me wane Abu suka kafa da mutum hamsin zasu Rika cin arzikinsa a kullum?
Amman Kash sun cusa musu bakin ciki, hassada, keta da zaluntar wadanda Basu jiba Basu gani ba. Allah ya kyauta’
Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=508617253273925&id=114506719351649
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.
You must log in to post a comment.