Assalamu alaikum barkanmu da asubahin lahadi, biyar ga watan Zulhijja, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da shida ga watan Yuli na shekarar dubu biyu da ashirin.
- Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bai wa ‘yan Nijeriya da ke zaune a kasashen ketare, shawarar su agaza domin ciyar da Nijeriya gaba, a shagulgulan da ake yi na ranar ‘yan kasa da ke kasashen ketare ta duniya bakidaya.
- Nijeriya ta kammala shirin kwaso ‘yan Nijeriya rukuni na shida daga Amurka zuwa gida Nijeriya.
- Gwamnatin Tarayya za ta maido da zirga-zirgar jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna daga ashirin da tara ga watan nan na Yuli.
- Sojojin sama na Nijeriya sun kai farmaki ta sama wani sansani na ‘yan bindiga da ke jihar Zamfara, suka kashe da dama daga cikinsu.
- Likitoci sun sake bai wa gwamnatin tarayya wa’adin nan da goma sha bakwai ga watan gobe, ko dai ta share musu hawaye ko su tsindima yajin aiki.
- An ta harbin juna har a kofar fadar Oba na Binin tsakanin ‘yan PDP da ‘yan APC da ke yakin neman zaben gwamnan jihar Edo.
- Majalisar Wakilai ta kaddamar da sabon littafin ajandar dokokinta, da ya mayar da hankali ga tattalin arziki, da tsaro, da aikin gona da lafiya.
- Hukumar Kare Hakkin Bil’Adama ta Kasa NHRC a takaice, ta soki yawan kai hare-hare da ake yi sassan kudancin jihar Kaduna.
- Gwamnatin jihar Kaduna ta fadada dokar da ta sa ta hana walwala ta sa’a ashirin da hudu a kullum a karamar hukumar Zangon Kataf, da ta Kauru, zuwa karamar hukumar Kaura da ta Jama’a saboda karuwar kai wa al’umomin yankunan hare-hare ana ta kashe na kashewa da raunata na raunatawa musamman cikin sa’o’i ashirin da hudu na baya-bayan nan.
- Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da kusan wata hudu ke nan suna jiran ariyas na sabon albashi.
- Yanzun wuraren karfe uku na dare, akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 438 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Legas 123
Kaduna 50
Ribas 40
Edo 37
Adamawa 25
Oyo 20
Nasarawa 16
Oshun 15
Inugu 15
Abuja 14
Ekiti 13
Ondo 13
Ebonyi 11
Katsina 10
Abiya 9
Delta 8
Kwara 4
Ogun 3
Kuros Ribas 3
Kano 3
Bauci 3
Yobe 2
Neja 1
Sakkwato 1
Jimillar da suka harbu 39,977
Jimillar da suka warke 16,978
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 856
Jimillar da ke jinya 22,173
Mu wayi gari lafiya.
Af! Ga wadanda suka ga rubutuna na ranar 25/7/2015 da na waiwaya jiya da ya cika shekara biyar cur, ga na rana mai kamar ta yau wato 26/7/2015 shi ma shekara biyar daidai da na rubuta shi kamar haka:
‘Yau da sassafe wani abokina soja mai jar hula ya kira ni a waya don mu gaisa. Na tambaye shi ko ya ga shawarar da na ba Baba Buhari jiya a fesbuk ta ya tsige su Buratai saboda ci gaba da kashe jama’a da kungiyar boko haram ke yi? Sai ya ce assha ai sai da Buhari ya binciki halayen Buratai tun yana NDA har zuwa yanzun kafin ya nada shi. Ya ce Buratai soja ne mai zuciyar soja ba shi da tsoro kuma ba ruwansa da rashawa. Ya ce da aka nada Buratai kananan sojoji suna ta murna saboda sun san in dai Buratai ne to kungiyar boko haram ta gama yawo. Ya ce manyan hafsoshin soja da suka zama gafiyoyi ne ba su ji dadin nadin Buratai ba saboda kwanan nan za su amayo dukiyar kasa da suka wawure. Wannan ita ce hirar da muka yi da abokina soja mai jar hula’
Sai dai ko jiya na ga wannan abokin nawa soja mai jar hula ya yi tsokaci a rubutuna yana sukar su Buratai.
Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a:
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2659970350942026&id=2356865571252507
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.
You must log in to post a comment.