Assalamu alaikum barkanmu da asubahin alhamis, goma sha bakwai ga watan Zulkida, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da tara ga watan Yuli, shekarar dubu biyu da ashirin.
- Jiya Majalisar Zartaswa ta Kasa ta yi taron da ta saba yi duk mako karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari, har aka yi tsit na minti guda domin juyayin rashin da aka yi na Inuwar Abdulkadir. A abubuwan da aka cimmawa har da amince wa kwalejin foliteknik ta Kaduna ta kulla wata yarjejeniya ta fahimtar juna da wani kamfani, da zai yi shekara daya yana gyaran wajen kwanan dalibai a naira miliyan dari bakwai da saba’in da hudu, da dubu dari biyu da sittin da hudu, bayan ya gyara, zai gudanar da wuraren kwanan na tsawon shekara goma sha hudu, don mayar da kudinsa.
- Ministan Ilimi Adamu Adamu ya ce daliban da ke makarantun sakandare na gwamnatin tarayya na hadin kai da aka fi sani da Unity Schools, ba su a rubuta jarabar WAEC ta yammacin Afirka da aka tsara farawa a farkon watan gobe saboda kwaronabairos. Ya ce da a yi sakacin da dalibai za su harbu, gara a hakura ko da za su yi shekara daya ne a gida.
- ‘Yan bindiga a babur fiye da saba’in suka je kauyukan da ke tsakanin jihar Sakkwato da jihar Zamfara, suka kashe na kashewa, suka sace na sacewa har da mata fiye da ashirin duk sun kwashe su, suka hada da dabbobi da hatsi. Wadanda suka tsira na wasu garuruwan suna gudun hijira.
- Wasu ‘yan kungiyar Boko Haram sun yi wa wasu sojojin Nijeriya kwanton-bauna a hanyar Maiduguri zuwa Damboa, inda BIbisi Hausa suka ba da rahoton cewa wata majiya ta ce sun kashe sojoji goma sha tara, wasu suka ji rauni, amma shalkwatar tsaro ta ce sojoji biyu aka kashe, su kuma suka kashe ‘yan kungiyar Boko Haram su goma sha bakwai.
- Wasu ‘yan bindiga sun kashe Hakimin Bajida da ke karamar hukumar Fakai a jihar Kabbi Alhaji Musa Muhamnad Bahago.
- Jiya tasoshin jiragen sama na Legas da Abuja suka bari jirage suka dawo da zirga-zirga ta cikin gida, da kamfanonin jiragen sama guda biyar.
- Iyalan Magu sun ce bai kwashe kayansa daga gidan da yake ciki na gwamnati kamar yadda ake ta rade-radi ba.
- Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi har ma da jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, suna ci gaba da korafin har yau ba su ga ariyas ba.
- Jiya da daddare kafin in kwanta bacci akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos su dari hudu da sittin a jihohi da alkaluma kamar haka:
Legas 150
Ribas 49
Oyo 43
Delta 38
Abuja 26
Anambra 20
Kano 20
Filato 18
Edo 14
Bayelsa 13
Inugu 13
Oshun 12
Kwara 10
Barno 8
Ogun 7
Kaduna 6
Imo 4
Bauci 3
Gwambe 3
Neja 2
Adamawa 1
Jimilar harbuwa 30,249
Jimilar warkuwa 12,373
Jimilar mutuwa 684
Jimilar jinyantuwa 17,192
Mu wayi gari lafiyuwa.
Afuwan!
Na lura a ‘yan kwanakin nan mutane na ta sa hotunan sojoji manya da kanana da suka riga mu gidan gaskiya sakamakon fafatawa da ko ‘yan bindiga ko ‘yan kungiyar Boko Haram. Da ke nuna sojojinmu na bukatar addu’a.
Za a iya leka rubutun labarun nawa na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.
You must log in to post a comment.