Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin asabar, ashirin da shida ga watan Zulkida, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyem halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha takwas ga watan Yuli na shekarar 2020.

  1. Shugaban Kasa Muhamdu Buhari na bai wa Keyamo umarnin ya share ‘yan majalisa ya yi aikin da ya sa shi na daukar aiki, sai shugabannin majalisun biyu suka ruga wajen shugaban kasa, suna fitowa daga wajensa sai aka ji shugaban kasa yana gargadi ga ministoci da ma’aikatu da hukumomi cewa daga yanzun ba zai sake yarda a raina ko yi wa ‘yan majalisar dokoki wargi ba.
  2. Ana nan ana ta tirka-tirka tsakanin shugabannin hukumar raya yankin Neja Delta NDDC da wacce aka taba ba rikon hukumar Joi Nunieh da ministan yankin Akpabio, da ‘yan majalisar wakilai da gwamna Wike da hukumar ‘yan sanda. Ana zargin ana ta wawurar kudaden hukumar wurjanjan.
  3. Magu ya ce ba shi ba daukar matakin shari’a tsakaninsa da gwamnatin tarayya ko hukumar ‘yan sanda tare da alkawarin ci gaba da ba da hadin kai ga bincikensa da ake kan yi.
  4. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nuna farin cikinsa da aka nada dan Nijerya Farfesa Charles Egbu a matsayin shugaban jami’ar Leeds Trinity da ke Ingila.
  5. Gwamnatin Tarayya ta bai wa masu makarantu nan da ranar 29 ga watan nan su cika ka’idoji da sharuddan bude makarantu a ranar da gwamnati za ta sanar nan gaba.
  6. Gwamnatin Tarayya ta tsara jirage guda uku da za su kwaso ‘yan Nijeriya daga Amurka ranar 17 da 28 da 31 duk ga watan nan. Zuwa yanzun an kwaso ‘yan Nijeriya 487 daga Amurka.
  7. An ta jita-jitar daga jiya ma’aikatan kwalejojin foliteknik na gwamnatin tarayya za su soma jin dilin-dilin na ariyas da suka shekara daya da wata uku suna jira, amma har zuwa wurare karfe karfe uku na dare da nake wannan rubutu ban samu rahoton wani ya ji dilin-dilin din ba.
  8. Zuwa karfe ukun na dare da nake wannan rubutu akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos mutum 600 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 129
Abuja 118
Oyo 87
Kano 55
Binuwai 42
Inugu 35
Kwara 28
Imo 16
Ogun 13
Kaduna 12
Ondo 12
Delta 11
Edo 11
Filato 8
Nasarawa 6
Ekiti 6
Barno 4
Abiya 4
Gwambe 3

Jimillar wadanda suka harbu 35,454
Jimillar wadanda suka warke 14,633
Wadanda suka riga mu gidan gaskiya 772
Wadanda ke jinya 19,994

Mu wayi gari lafiya.

Af! Ina cikin zamana sai in ji an jefa ni a cikin wani dandali na soshiyal midiya. Ni kuma asubah na yi sai in jefa rubutun labarun da nake yi kullum, dandanan sai ka ga an ciccibo ni an wurgo ni waje daga dandalin. Ko jiya an yo wurgi da ni waje daga wani dandali da ban san wa ya ciccibe ni ya jefa ni ciki ba wai shi Dandalin Karatu. To an taba yin dakin karatu ba a yi tanadin wajen samun labarun duniya ba?

Za a iya leka rubutun labarun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

https://www.facebook.com/2356865571252507/posts/2653537131585348/
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta