Sharhin Bayan Labarai…

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin laraba, goma sha shida ga watan Zulkida, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da takwas ga watan Yuli na shekarar dubu biyu da ashirin.

 1. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa ta EFCC Ibrahim Magu a daidai lokacin da fadar shugaban kasa ke masa tambayoyi a kan zargin da ake masa na rashawa da sauran laifuka har guda ashirin da biyu. An ce an ga Magun na kwashe kayansa daga gidan gwamnati da yake ciki da ke Maitama a Abuja, kuma an ga jami’an tsaro na bincike a gidansa na kansa da ke Kari.
 2. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sake nada Farfesa Dambatta a matsayin babban mataimakin shugaban hukumar sadarwa ta kasa NCC.
 3. Rashin halartar alkali da ke shari’ar su Hamisu Wadume ta sanya jinkirta shari’ar tasu.
 4. An ci gaba da neman gawawwakin wadanda wasu ‘yan bindiga a babur su fiye da dari biyu suka kashe a Batsari ta jihar Katsina ana musu jana’iza. An bayyana cewa sun kashe fiye da mutum goma sha biyar a gona.
 5. Ministan Kwadago Ngige ya ba ‘yan majalisar dokoki hakuri a kan sa-in-sar da suka yi da karamin ministansa Keyamo a kan shirin nan na daukar mutum dubu dari bakwai da saba’in da hudu aiki, sai dai shi Keyamo ya ce ba gudu ba ja da baya ba zai yi abin da ‘yan majalisar suke so na kankane tsara shirin ba, sai fa in shugaban kasa ne ya ba shi umarnin ya sakar musu. Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawal ya ce sun ma rusa kwamiti mai mutum ashirin wadanda su Keyamo suka zabo don aiwatar da shirin.
 6. Majalisar Dattawa ta amince da kudirin dokar daure duk wani lakcara da ya ci zarafin wata daliba, ta hanyar lalata, ko yi mata batsa ko da a rubuce ne ta wasaf ko fesbuk, ko dai wani wasan banza ko kwarkwasa, daurin shekara goma sha hudu ko tarar naira miliyan dari biyar ko a hada wa lakcaran duka biyun.
 7. Wasu ‘yan kungiyar Boko Haram sun kai hari Konduga da ke jihar Barno jiya da almuru, amma sojoji sun ce sun dakile harin.
 8. ‘Yan Majalisar Wakilai na shirin bincikar Kamfanin Mai Na Kasa NNPC saboda cire wata dala biliyan daya da ‘yan kai daga wani asusu na kamfanin gas na LNG.
 9. Allah Ya yi wa Aminu Adisa shugaban ma’aikatan gidan gwamnati na jihar Kwara rasuwar sakamakon harbuwa da kwaronabairos.
 10. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata uku ke nan suna jiran ariyas na sabon albashi ba amo ba labari. Har wasunsu sun ce sun fara cire rai, watakila idan Baba Buhari ya gama wa’adinsa wata gwamnatin ta hau, ta biya su.
 11. Jiya kafin in kwanta bacci da daddare, akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos su dari biyar da uku a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 153
Ondo 76
Edo 54
Abuja 41
Inugu 37
Ribas 30
Binuwai 24
Oshun 20
Kaduna 15
Kwara 13
Abiya 9
Barno 8
Filato 6
Taraba 5
Ogun 3
Kano 3
Kabbi 2
Nasarawa 2
Bayelsa 1
Gwambe 1

Wadanda suka harbu 29,879
Wadanda suka warke 12,108
Wadanda suka riga mu gidan gaskiya 669
Wadanda ke jinya 17,102

Mu wayi gari lafiya.

Af! A rana mai kamar ta yau shekara hudu baya, wato ranar 8 ga watan Yuli na shekarar dubu biyu da goma sha shida, na yi wannan rubutu kamar yadda na saba yi kullum:

‘Jama’a da fatan mun wayi gari lafiya kuma yau juma’a mu ci gaba da addu’a. A shekara 25 da na yi ina koyar da Hausa a makarantu daban-daban ba karamin wulakanci na sha ba saboda ina koyar da Hausa. Saboda irin kallon hadarin kaji da ake yi wa Hausa da malaman Hausa a yawancin makarantun kasar nan.To irin wannan wulakanci da na sha na tattaro su na rubuta su a jaridar Leadership/Lidaship ta Hausa ta yau juma’a da za ta fito da safiyar nan. Wasu sun ce ina yi wa Jaridar talla a fesbuk nawa suke biyan kudin talla? To ni a shekaru uku da na yi ina yi wa Jaridar rubutu, ba ta taba ba ni ko sisi ba. Editan ma ban taba ganinsa ba sai a hoto. Kuma ai wanda yake yi da kai, da shi kake yi. A duk lokacin da na yi rubutu na tura, za a ajiye rubutun wasu a buga nawa. Akwai wasu jaridun da nake turawa rubutu suke jafa rubutun nawa a kwandon shara.Ko a buga in ga an yi karambani an bata mun rubutun. Tunda na kira su a waya in ji dalili na ji ana mun balbalin bala’i anà ce mun ba ni kadai ne marubuci ba kuma na cika neman suna in tsaya a jarida daya mana, sai na tsayar da hankalina ga Jaridar Lidaship. Ita ma Mujallar Muryar Arewa editanta da kan shi yakan yi mun waya ko akwai rubutu da zan tura musu su buga. Su ma ba wanda ya taba ba ni ko taro. Sai Jaridar Almizan ita ma editanta ya taba kirana a waya in dinga musu rubutu a jaridar tasu da ke fitowa duk juma’a. Saboda haka duk Jarida ko Mujallar da ta buga rubutuna ina mata talla a fesbuk don a saya. Godiya ga Abdulrazak Yahuza Jere da Dahiru Lawal da Al-Amin Ciroma da Kabir Assada. Su suke tsayin daka wajen buga rubuce-rubucena a jaridar Lidaship da mujallar Muryar Arewa’

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta