Shan Paracetamol Ba Bisa Ka’ida Ba Na Lalata Hanta – Likita

Wata fitacciyar likita, Esther Oke ta baiyana cewa shan ƙwayoyin maganin paracetamol ba bisa ƙa’ida ba babban haɗari ne ga lafiyar ɗan-adam.

Oke ta baiyana cewa ƴan Nijeriya da dama sun ɗauki tsawon shekaru su na shan paracetamol ba bisa ƙa’ida ba sakamakon jahilci.

Ta yi ƙarin bayani cewa irin waɗannan magungunan masu rage raɗaɗi na ɗauke da sinadari mai ƙarfi na paracetamol wanda ya ke lalata hantar ɗan-adam idan a na shan shi ba tare da ƙa’ida ba.

“Shan ƙwayoyi kamar guda 3 a maimakon 2 da wasu su ke yi ya saɓawa yadda ƙa’idar shan magani da duniya ta amince da ita.

“Bincike ya nuna cewa ƙwayoyi biyu na magani a ka yarda a sha kuma sau uku a ranar har zuwa kwanakin da likita ya rubuta,” ta yi gargaɗi.

Ta kuma bada shawarar cewa kada mutane su sha magunguna sai da sahalewar ƙwararren likita.

-Daily Nigerian.

Labarai Makamanta