Shakar ‘Yanci: Buhari Ya Taya Fasinjojin Jirgi Murna

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya taya fasinjojin jirgin kasa da kungiyar Boko Haram ta sako da yammacin Laraba murna.

Cikin wani sako na Tiwita da ya wallafa a shafinsa, shugaban ya ce, “Na yi maraba kuma na yi murna sosai da ba ji a sako sauran fasinjoji 23 na jirgin kasa da ‘yan ta’addan Boko Haram suka yi garkuwa da su, kuma kamar sauran ‘yan Najeriya, ni ma na ji dadin wannan labarin kuma muna alfahari da ayyukan da dakarun tsaron kasarmu suka yi.”

Ya kuma taya iyalan wadanda aka sakon murnar sake ganin ‘yan uwansu.

“Na jaddadawa jami’an tsaronmu da hukumomin da ke binciken bayanan sirri cewa ayyukan da muke yi na daidaita tsaron kasarmu na ci gaba, kuma ya kamata su jajirce wajen magance matsalolin ta’addanci da na barayin daji da kuma na satar mutane domin karbar kudin fansa a fadin kasar. Tilas mu ci gaba da aiki domin kwato dukkan yankunan kasarmu daga hannayen miyagu.”.

Labarai Makamanta