Sauya Takardun Naira: Za A Sanya Idanu Kan Masu Kai Kudi Banki

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministar tattalin arziki, kasafi da tsare-tsaren kudi ta Najeriya, Zainab Shamsuna Ahmed tayi karin haske game da sababbin kudi da za a buga.

A wani bayani da aka fitar a shafin LinkedIn a ranar Alhamis, an fahimci ba haka nan za a kyale mutane su rika maida kudin hannunsu cikin bankuna ba, ba tare da sa ido ba musanman daga Hukumar EFCC.

Ministar tace za a hukunta duk bankin da ya sabawa ka’idojojin da aka gindaya, Ministar ta bayyana cewar jami’an hukumar EFCC da babban bankin Najeriya za su riƙa lura da duk kudin da suke shiga asusun jama’a.

Zainab Shamsuna Ahmed ta ƙara da cewa daga yanzu babban bankin Najeriya watau CBN zai rage adadin takardun kudin da yake bugawa lokaci zuwa lokaci.

A farkon shekarar 2023 ake tsammanin Gwamnan babban Banki CBN zai fitar da sababbin tsare-tsare da za a bi wajen ganin jama’a sun rage yawo da kudi a hannunsu.

Labarai Makamanta