Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Majalisar wakilai ta tarayya ta umurci babban sufetan ‘yan sandan kasar ya kai mata gwamnan babban bankin kasar nan da ranar Talata mai zuwa.
Majalisar ta yanke wannan hukuncin ne bayan ta gayyaci gwamnan babban bankin har sau biyu ba ya zuwa.
Wani rahoto na cewa ‘yan majalisar suna so ne su ji daga bakin gwamnan dalilin da ya sa ba za a kara wa’adin daina amfani da tsofaffin takardun naira ba, wadanda bankin ya ce za su daina aiki daga ranar 31 ga wannan wata na Janairu.
‘Yan majalisar sun kai har wuya ne sakamakon gazawar gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele wajen bayyana a gaban wani kwamiti na musamman da majalisar wakilan ta kafa.
Kasancewar har sau biyu kwamitin yana sa lokaci, amma gwamnan babban bankin ya bar su suna jiran gawon shanu… shi bai je ba bai kuma tura wakili ba, wato ba wan ba kani…ga shi kamar yadda ‘yan majalisar ke cewa sun zaku su ji daga bakinsa ko wane dalili ne zai hana kara wa’adin daina amfani da tsoffin takardun kudin da bankin ya bayar, wato ranar 31 ga wannan wata na Janairu.
Kazalika kwamitin ya gana da shugabannin bankunan kasuwanci da ke Najeriya, duka dai da nufin jin ta bankin su inda gaskiyar maganar take game da karancin da ake fama da shi na sabbin takardun kudin.
You must log in to post a comment.