Sauya Takardun Naira: Ba Ma Tare Da Babban Banki – Ganduje

Gwamnonin Najeriya karkashin jam’iyyar APC mai mulin kasar sun bayyana wa Shugaba Muhammadu Buhari cewa manufar gwamantinsa ta sauyin fasalin takardun naira 200 da 500 da kuma 1,000 za ta haifar da tarin matsaloli.

Gwamnonin sun ce wannan ne yasa suka kuduri aniyar komawa jihohinsu domin fadakar da al’umominsu cewa jam’iyarsu ta APC ba ta da hannu ko kadan wajen fito da wannan manufar.

Bayan wata ganawa da gwamnonin suka yi da shugaban kasar, gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya shaida wa BBC cewa:

“Wannan ba ajandar APC ba ce, ajanda ce ta wadanda suka zagaye shugaban kasa, da kuma shi gwamnan babban bankin Najeriya wanda ka san ya nemi ya zama shugaban kasa amma abin ya lalace. Shi yasa suke son ko dai zaben nan ba a yi shi ba, ko kuma wata jam’iyyar ta lashe shi.”

Kan ko gwamnonin za su yi hannu riga da shugaban kasa kan wannan manufar, sai Gwamna Ganduje ya ce:

“A’a, mu muna hannun riga da wannan tsari na canjin kudi na gwamnan babban banki da kuma wadanda suka zagaye shugaban kasa.”

Labarai Makamanta