Gwamnonin sun hada da Nasir El-Rufa’i na Kaduna da Yahya Bello na Kogi da kuma Bello Mutawalle na Zamfara.
Gwamnonin na neman kotun da ta ayyana wannan shirin sauya kudin na CBN karkashin umarnin shugaba Muhammad Buhari a matsayin wanda ya yi hannun-riga da kundin tsarin mulkin kasar na sherkarar 1999 ( da aka yi wa gyaran fuska) da kuma dokokin bankin Najeriya na shekarar 2007.
Kazalika gwamnonin na son kotun kolin ta yi watsi da wa’adin da gwamnatin tarayya ta kayyade na daina amfani da tsoffin takardun Naira da suka hada da Naira 1000 da 500 da kuma 200, inda suka ce, wannan wa’adin ya saba wa sashi na 20 sakin layi na (3) na dokokin babban bankin kasar na 2007.
A makon jiya, gwamnonin na jam’iyyar APC mai mulki suka gana da shugaba Buhari, inda suka roke shi da ya bari a ci gaba da amfani da tsoffi da sabbin takardun na Naira, yayin da shugaban ya nemi su ba shi kwanaki bakwai domin nazari kan bukatarsu.
Shirin na sauya wa Naira fasali ya janyo tayar da jijiyoyin wuya a Najeriya mussamman ganin yadda ya haddasa karancin takardun kudi tsakanin al’umma.
You must log in to post a comment.