Sauya Shekar ‘Yan Siyasa Na Iya Haifar Da Rikici Nan Gaba – Abdulsalami Abubakar

Tsohon Shugaban Kasa na mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya) ya yi gargadi game da yawaitar sauya sheka da ‘yan siyasa ke yi, yana mai cewa hakan zai haifar da rudani da rigingimun da za su kara haifar da zullumi a kasa.

Tsohon Shugaban, a yayin kaddamar da shirin samar da zaman lafiya da hadin kan tsaro da gwamnonin jihohi 36 suka yi jiya a Abuja, ya yi gargadi kan yawaitar sauya sheka da ‘yan siyasa ke yi daga wata jam’iyyar siyasa zuwa wata.

Yana tsokaci ne game da yadda ‘yan siyasa suka sake lale a tafiyar siyasarsu gabanin babban zaben 2023; inda wadansu daga cikinsu, musamman gwamnoni da ‘yan majalisa suke canza jam’iyya.

Akalla gwamnoni uku ne suka sauya sheka daga Jam’iyyar hamayya ta PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki tun a watan Nuwambar bara lokacin da gwamnan Jihar Ebonyi, Cif Dave Umahi, ya fice daga jam’iyyar PDP ya koma APC. Sauran wadanda suka sauya sheka sun hada da Gwamnonin jihohin Kuros Riba, Farfesa Ben Ayade da na Jihar Zamfara, Alhaji Bello Matawalle.

Har ila yau, a wajen taron, Ofishin Jakadancin Burtaniya a Najeriya, ya yi gargadin cewa rikicin da ke fuskantar Najeriya, idan ba a hanzarta magance shi ba zai iya hargitsa tsarin dimokoradiyyar kasar da ma babban zaben 2023.

Har ila yau, ofishin ya bukaci da a yi garambawul cikin gaggawa a rundunonin soja da na ‘yan sandan Najeriya, yana mai jaddada cewa amfani da karfin soja da ‘yan sanda kadai ba zai zama mafita wajen magance kalubalen tsaro da ke addabar Najeriya ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply