Sauya Sheka: Abdullahi Adamu Ya Koka Da Yadda Ake Barin APC

Shugaban jam’iyyar APC mai mulki Sanata Abdullahi Adamu ya ce ya damu matuka, kan yadda ake barin jam’iyyar.

Sanatoci bakwai ne suka sauya sheka daga APC zuwa wasu jam’iyyun, bayan sun kasa samun tikitin tsayawa takara a jam’iyyar a zaben 2023.

Sanatocin da suka fice daga APCn sun hada da tsohon gwamnan Kano Ibrahim Shekarau, da Yahaya Abdullahi daga jihar Kebbi, da Dauda Jika daga jihar Bauchi da kuma Ahmad Babba Kaita daga jihar Katsina.

Sauran sun hada da Lawal Yahaya Gamau daga Bauchi, sai kuma Francis Alimikhena daga jihar Edo.

Da yake magana da manema labarai bayan wata ganawar sirri da Sanatocin jam’iyyar, Adamu ya ce akwai takaici irin yadda yan majalisar ke ficewa daga jam’iyyar.

” Ban damu da abinda ke faruwa a wata jam’iyya ba, damuwa ta itace abinda ke faruwa a jam’iyyata.”

” Babu Shugaba nagari da ba zai damu ba idan ya rasa mamba ko da daya ne a jam’iyyarsa, ballantana ayi maganar mamba biyu, ko uku.”, in ji Adamu.

Labarai Makamanta