Saura Ƙiris Abubuwa Su Daidaita A Najeriya – Osinbajo

Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbaj a ranar Lahadi, ya karfafa wa ‘yan Nijeriya gwiwa da cewa “su yi babban fatan cewa nan bada dade wa ba, abubuwa za su daidaita a kasar nan” kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Osinbajo ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da yayi da manema labarai bayan kammala bikin Ista a ranar Lahadi a Aso Villa Chapel.

A cewar wata sanarwa daga babban hadiminsa na musamman kan yada labarai da, Laolu Akande, Osinbajo ya yi addu’ar cewa Najeriya za ta dandana alheri da rahamar Allah.

Labarai Makamanta