Saudiyya Ta Amince A Buɗe Wuraren Shan Shisha

An amince a sha shisha a wuraren shan gahawa a Saudiyya daga ranar Litinin yayin da ake sassauta dokar kullen korona a ƙasar.

Ma’aikatar kula da birane da karkara ta amince a sayar da shisha ga waɗanda aka yi wa rigakafin korona, kamar yadda kamfanin dillacin labaran ƙasar na SPA ya ruwaito.

Amma za a dinga shan shishar ne a sarari yayin da aka haramta sha wuraren da ake cin abinci.

Saudiyya ta rufe gidajen cin abinci da shan gahawa domin rage bazuwar korona.

Labarai Makamanta