Saudiyya: An Damƙe Mutumin Da Ya Yi Yunƙurin Kashe Limamin Ka’abah

Rahotanni daga ƙasar Saudiyya sun bayyana cewa a ranar Jumu’a yayin gudanar da huɗuba, wani mutumi sanye da harami yayi ƙoƙarin hallaka ɗaya daga cikin limaman masallacin Ka’aba.

Mutumin yayi ƙoƙarin isa ga limamin amma sai jami’an tsaro suka farga kuma suka kama shi nan take.

Hukumar dake kula da manyan masallatai biyu masu daraja ‘Haramain Sharifain’ ita ce ta bayyana haka a shafinta na kafar sada zumunta Facebook.

Hukumar tace anyi yunƙurin kashe Sheikh Baleelah a dai-dai lokacin da yake huɗubar sallar jumu’a a masallacin ka’aba. Hakanan hukumar Haramain Sharufai ta sanya bidiyon yadda mutumin yayi ƙoƙarin kutsawa zuwa ga limamin da yadda jami’an tsaro suka yi gaggawar damƙe shi a shafinta na kafar sada zumunta.

A jawabin da hukumar tayi tace: “Wani mutumi ya tunkari inda mumbarin liman yake a masallacin ka’aba riƙe da makami, amma jami’an tsaro sun yi nasarar damƙe shi.”

Labarai Makamanta