Satar Mai: Muna Asarar Dala Biliyan Biyu Duk Wata – Gwamnatin Tarayya

Rahotannin dake shigo mana daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ce, tana asarar kusan Dala biliyan biyu kowanne wata saboda satar ɗanyen man da ake yi a yankin Neja Delta.

Shugaban kamfanin man NNPC na ƙasa Alhaji Mele Kyari ya bayyana haka lokacin da tawagar ministan mai Timipriye Sylva ta kai ziyara ga gwamnan Delta Ifeanyi Okowa a fadar gwamnatinsa da ke Asaba babban birnin jihar.

Kyari ya ce, sakamakon wannan kazamin satar da ke gudana, Najeriya ba ta iya cike gurbin da kungiyar kasashe masu arzikin man fetur OPEC ta ba ta na fitar da man zuwa kasuwannin duniya kowacce rana.

Shugaban kamfanin ya ce abin takaici ne yadda wannan matsalar ta hana Najeriya samar da gangar mai kusan miliyan biyu da OPEC ke bukata, ganin yadda kasar ke samar da kasa da ganga miliyan daya da rabi kowacce rana.

Kyari ya ce bayan asarar dukiyar da Najeriya ke yi, kasar kuma na fuskantar babbar matsalar gurbata muhalli a yankunan da ake satar danyan man.

Labarai Makamanta