Satar Ibori: Kuɗin Da Birtaniya Ta Dawo Da Su Na Jihar Delta Ne – Majalisa

Majalisar wakilan Najeriya ta tabbatar da kudi fam miliyan 3.4 da aka dawo dasu daga Burtaniya da tsohon Gwamnan Jihar James Ibori ya sace mallakar gwamnatin jihar Delta ne, ba Gwamnatin Tarayya ba.

Majalisar wakilan ta nemi gwamnatin tarayya ta hannun ministan kudi da ta dakatar da rabon kudin da aka kwato a hannun tsohon gwamnan Delta, cikin gaggawa ba tare da wani ɓata lokaci ba.

Majalisar ta cimma wannan matsayar ne bayan kudirin da ‘yan majalisa guda tara karkashin jagorancin shugaban marasa rinjaye na majalisar, Hon. Ndudi Elumelu, suka gabatar a ya yin zamanta na ranar Laraba.

Majalisar kuma ta nemi ma’aikatar kudi da kuma ofishin ministan shari’a na kasa da su gabatar mata da dukkanin wasu takardu dangane da kudaden da aka dawo da su.

Masu goyon bayan kudirin sun hada da: Ndudi Elumel; Hon. Victor Nwokolo; Hon. Nicholas Motu; Hon. Leo Ogor; Hon. Ossai Ossai; Hon. Julius Pondi; Hon. Ben Rollands Igbakpa; Hon. Hon. Efe Afe; Hon. Thomas Ereyitomi da Hon. Francis E. Waive.

Yayin da yake gabatar da kudin mai taken “Bukatar gaggawa ta dakatar da rabon kudaden da aka kwato daga hannun tsohon gwamnan jihar Delta” Mr Elumelu ya kafa hujja da cewa irin hakan ya taba faruwa inda aka mayar da kudaden sata ga jihohin Abia da Bayelsa.

Ya bayyana cewa: “Kuɗin kimanin fam miliyan 4.3 na sata da aka kwato a hannun tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori, ana kan turasu asusun gwamnatin tarayya batare da neman hurumin gwamnatin Jihar Delta ko majalisa ba nan da sati biyu.

Kudaden da ake fadin an dawo da su mallakin mutanen jihar Delta ne saboda haka yakamata ace an dawo da su asusun jihar domin yin ayyukan cigaba,” a cewarsa Majalisar ta damu kan cewa idan aka bar gwamnatin tarayya tayi amfani da kudin ba tare da hurumin mutanen jihar Delta ba, za’a tauye musu hakkin su na cin moriyar albarkatun su.

Daga dukkan alamu da bayanai daga gwamnatin jihar Delta sun nuna hakikanin kudin yakai fam miliyan 6.2. Sannan gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa fam miliyan 6.2 aka sanya ba fam miliyan 4.3 ba kamar yadda aka fada.

Majalisa tayi amanna cewa idan har gwamnatin tarayya ba ta daina taba kudaden ba, to tabbas kudaden da aka kwato zasuyi batan dabo.

Domin Amincewa da kudirin, majalisa ta umurci kwamitin kudi, sharia, basussuka da kuma kudaden da aka kwato daya binciki lamarin cikin sati biyu sannan ya dawo ma majalisar.

Labarai Makamanta