Satar Fasaha: Kamfanin Coca-Cola Ya Maka Pop-Cola Kotu

Kamfanin Coca-Cola ya gurfanar da kamfanin Mamuda Beverages, masu yin Lemun Pop-cola a gaban Kotun ɗaukaka ƙara da ke Kano, bisa zargin satar fasaha.

Lemon Pop-cola dai kamfanin Mamuda Beverages ne ya ƙaddamar a cikin watan Yunin shekarar nan.

Tun da farko kwafin ƙarar da kamfanin na Coca-Cola ya gabatar wa kotun, ya yi ƙorafin yadda kamfanin Mamuda Beverages ya saci fasahar zanen da ke jikin kwalbar Coca-Cola, da a turance ake kira da RIBBON ya yi matuƙar kama da wanda ya ke jikin Coca-Cola, tare kuma da kwaikwayon sunan na Coca-Cola inda aka fitar da Pop-cola.

Haka kuma kamfanin na Coca-Cola ya sanar wa kotun cewa shi ke da haƙƙin mallakar sunansa tareda zanen na RIBBON a ciki da wajen Najeriya.

Kamfanin ya ƙara da cewa waɗannan siffofi mallakin kuma sun yi amfani da su a kasashen duniya daban-daban ciki har da Najeriya.

Hakazalika kamfanin na Coca-Cola ya buƙaci kotun da ta haramtawa kamfanin Pop-cola yin amfani da wadannan siffofi a manyam allunan talla da motocin da ke sufurin lemon Pop-cola, sakamakon yin amfani da siffofin da ba hakkin mallakarsa ba ne.

A nasa ɓangaren lauyan da ke kare kamfanin Mamuda Beverages, George Ogunyomi, ya buƙaci kotun da ta ba shi lokaci domin yin martani ga wannan ƙorafin satar fasaha da kamfanin ya yi musu.

A ƙarshe mai shari’a Muhammad Nasir Yunusa, ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 11 ga watan Disamban 2021

Labarai Makamanta