Satar Ɗalibai: Da A Kudu Ne Da Tuni An Ɗauki Mataki – Mansura Isa

Tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa,Mansurah Isah ta bayyana takaicinta kan yanda aka rasa samun nuna halin damuwa da sace dalibai da akw a Arewa.

Ta tambayi cewa shin ‘yan Legas ne kadai zasu iya yakar gwamnatin Najeriya da kawo Canji, saboda Su kadai gwamnati take jin tsoro.

Tace suna fitowa su bayyana samuwarsu ba tare da fargaba ba, kuma kana taba daya daga cikinsu kamar ka taba dukansu ne, basa yacewa juna baya.

Tace babu Munafurci ba Kyashi ba bakin ciki. Tace ana magana yanzu, ko wani abune ya sameka, musulmi dan uwanka ne zai fara cewa Allah kara, kadan ma ya gani, Allah kara mishi Musiba. Tace da sune aka sace yara a Makaranta, ai da yanzu sun hana gwamnati bacci, da sun ta yayata abin a shafukan sada zumunta ta yanda kasar Amurka tuni zata shiga maganar.

Mansurah ta bayyana cewa gaskiya tana cikin damuwa sosai kan wannan lamari. Ta kara da cewa, yanzu maganar ‘yan fim ce kawai zata sa a hade kai ai ta cece-kuce akanta.

Mansurah tace bafa wanda zai taimakemu sai mun tashi mun taimaki kanmu. Tace tana kira da a fito a yi magana kan matsalolin Arewa.

Labarai Makamanta