Satar Ɗalibai: Atiku Ya Yi Kiran Sa Dokar Ta Baci Bangaren Ilimi

Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa kuma ɗan takarar Shugabancin ƙasa ƙarƙashin jam’iyyar adawa ta PDP Wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar, ya nuna tsananin damuwa da takaici dangane da yawaitar sace sacen ɗalibai da ake samu a makarantun Gwamnati a yankin Arewa.

Jagoran adawa ya sake jaddada kira a saka dokar taɓaci a harkar ilimi biyo bayan sace ɗaliban firamare a Jihar Kaduna.

Da hantsin ranar Litinin ne wasu ‘yan bindiga suka kutsa makarantar firamare ta Rema da ke Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari, inda suka yi awon gaba da ɗalibai da malamai, waɗanda ba a san adadinsu ba.

Atiku ya ce ya kamata gwamnati ta tura jami’an tsaro kowace makaranta a yankunan da ke fama da hare-haren ‘yan fashin daji da ke yin garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa. .

“Yayin da aka sake samun wani hari kan makaranta a Kaduna, ina sake jaddada kira ga gwamnatin tarayya ta saka dokar ta-ɓaci kan ilimi sannan a tura jami’an tsaro su yi gadin dukkan makarantu a yankunan da abin ya shafa,” in jis hi.

“Wajibi ne kuma mu daina biyan kuɗin fansa haka kawai. Wani sauƙi ne (biyan kuɗin fansa) na ɗan lokaci wanda zai haifar da babbar matsala a nan gaba.

“A matsayinmu na ƙasa, dole ne mu tabbatar da doka da oda ko kuma mu bar wa jikokinmu gadon matsaloli. Allah ya kiyaye hakan.”

Labarai Makamanta