Sarkin Musulmi Ya Yi Kiran Fara Duban Jinjirin Watan Rajab

Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Nijeriya, NSCIA, ta ce al’ummar musulmi su fara duba sabon watan Rajab a kalandar musulunci daga ranar yau Juma’a.

Sanarwar ta NSCIA da sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ke jagoranta ta ce Juma’a ce zata kasance 29 ga watan Jumadal Akhira wanda zai yi dai-dai da 12 ga watan Fabrairun shekarar 2021.

Kazalika, sanarwar ta umurci al’umma da su kai rahoton ganin Jinjirin watan ga dagaci ko mai unguwa mafi kusa da su domin isar da sakon da ganin jinjirin watan ga mai alfarma Sarkin Musulmi.

Sanarwar wacce Wazirin Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Wali Junaidu ya saka wa hannu ta ce a fara duban jinjirin watan bayan faduwar rana.

Watan Rajab shine na wata na Bakwai cikin jerin watannin da ke kalandar Musulunci ta Hijra, mai biye masa kuma shine watan Sha’aban sai kuma Ramadan watan azumi.

Labarai Makamanta