Sarkin Musulmi Ya Kalubalanci Miyyeti Allah Ta Taimaka Kan Matsalar Tsaro

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya buƙaci shugabannin ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah da su taimaka wa gwamnatin tarayya wajen magance matsalar tsaron da ƙasar ke fuskanta.

Yayin da yake magana a Abuja babban birnin tarayya lokacin bikin rantsar da sabbin shugabannin ƙungiyar, sarkin Musulmin ya ce al’ummar Fulani makiyaya masu son zaman lafiya ne da kaunar juna.

Muhammad Sa’ad Abubakar III wanda shi ne shugaban Majalisar Ƙoli ta Addinin Musulunci, ya yi kira ga sabbin shugabannin ƙungiyar da su yi ƙoƙarin taimaka wa gwamnati wajen magance matsalar tsaro da ƙasar ke fuskanta.

Najeriya musamman yankin Arewa maso yamma na fuskantar gagarumar matsala ta rashin tsaro da ake dangatashi ga Fulani makiyaya masu ikirarin ɗaukar fansa akan abin da suka kira cutar dasu da ake yi a yankin.

Matsalar tsaron ta yi sanadiyar mutuwar mutane masu yawa da tursasa jama’a da dama barin muhallin su a yankin gami da tayar da ƙauyuka masu yawa a yankin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply