Sarkin Musulmi Ya Kalubalanci Buhari Da Gwamnoni Su Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Sultan Alhaji Sa’ad Abubakar III ya kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnoni da su kawo karshen rashin tsaro wanda ya daɗe yana addabar mutane a faɗin kasar nan cikin gaggawa ba tare da wani ɓata lokaci ba.

Sarkin Musulmin wanda shine shugaban majalisar koli ta al’amuran addinin Musulunci a Najeriya, yayi wannan jawabin ne a Sokoto bayan sallar idin karamar sallah da aka yi a ranar Alhamis da ta gabata.

“Muna kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da dukkan gwamnonin jihohi da su gaggauta kawo karshen rashin tsaro da ya addabi kasar nan nan take ba tare da wani jinkiri ba.

“A matsayinku na shugabanni, dole ne ku dage wurin sauke nauyin dake kanku na bada kariya ga al’umma. “A don haka, dole ne ku kara zagewa wurin ganin kun dawo da zaman lafiya a kasar nan irin wanda muka dade da sanin muna da shi.”

Sarkin Musulmin yayi kira ga Musulmi da su cigaba da yi wa shugabanni addu’a domin Allah ya basu damar daukar dawainiyar da ta hau kansu. Yayi kira ga Musulmi da su cigaba da bayyana halayyar karamci da kaunar juna wanda sallah ke nunawa.

“Yau babbar rana ce garemu ta murna, ku nuna soyayya, kauna, goyon baya kuma a yi mu’amala mai kyau.”

Labarai Makamanta