Sarkin Musulmi Ya Gargadi Buhari Kan Biyan Hakkin Malaman Jami’a

Mai Alfarma Sarkin musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya bukaci shugaba Buhari ya girmama yarjejeniyar da gwamnatinsa ta cimma da kungiyar malaman jami’o’i ASUU a shekarar 2020.

An ruwaito cewa Sarkin, wanda shine shugaban jami’ar Ibadan, ya yi wannan furucin ne a jami’ar ranar Laraba. Alhaji Sa’ad Abubakar ya nemi haka ne yayin da yake jawabi a wurin bikin yaye ɗalibai na jami’ar Ibadan karo na 73 tun bayan kafa makarantar.

Shugaba Buhari na cikin mahalarta taron, kuma ya samu wakilcin mataimakin sakataren hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC).

Sarkin musulmin ya kira yi gwamnatin tarayya ta tabbata ta yi duk me yuwuwa domin cika alkawarin dake cikin yarjejeniyar da suka cimma da Malaman domin gujewa jefa daliban jami’o’i cikin wata azaba ta wani yajin aiki.

“Ina kira ga Shugaba Buhari ya taimaka ya duba bukatar ASUU, mun ji labarin kungiyar ta baiwa gwamnati wa’adi bisa ga yarjejeniyarsu.” “Kun cimma matsaya tsakanin ku, to ya kamata a girmama wannan alkawurran, mutumin kirki yana cika alkawarin da ya ɗauka ga kowa.

A musulunci mun san Allah ba ya ɗaukar alkawari ya ƙi cikawa.” “Idan gwamnati ta ɗaukarwa ASUU wasu alƙawurra, Dan Allah ku taimaka ku cika musu, domin haka ne kaɗai zai sa jami’o’in mu su cigaba da aiki, kuma ɗaliban mu su cigaba da karatun su.”

Labarai Makamanta