Sarkin Kano Ya Kori Ɗan Majalisar Shi Saboda Taya Ganduje Murna

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito shine, Sarkin na Kano ya ɗauki matakin korar Alhaji Auwalu Maja Sirdin Sarkin Kano ne biyo bayan halartar walimar taya Ganduje murnar nasara a Kotu da ya yi.

Wani Bafade a fadar Sarkin wanda ya buƙaci a ɓoye sunan shi saboda tsaro, yace Auwalu Maja Sirdin Sarkin Kano Dattijo ne wanda ya lashe sama da shekaru 30 akan wannan matsayi, sarauta ce da marigayi Sarkin Kano Ado Bayero ya naɗa shi akai, ta kula da yi wa Dawaki ado.

Sarki Muhammadu Sunusi ll ya haramta wa ‘yan Majalisar fadar sa halartar dukkanin wani biki ko taro ba tare da izini daga gare shi ba, amma sai aka samu Alhaji Auwalu da halartar taron Ganduje ba tare da izinin mai Martaba ba, inji Bafaden.

Dangata tsakanin Gwamnan jihar Kano da mai Martaba Sarkin Kano na ƙara tsami, tun bayan goyon bayan da Sarkin ya nunawa tafiyar Kwankwaso akan zaɓen Gwamna da ya gabata, lamarin da ya haifar da kacaccala masarautar Kano zuwa masarautu biyar.

Related posts