Sarki Salman Ya Yi Wa Buhari Ta’aziyar Rasuwar Shugaban Dakarun Soji

Sarki Salman Ibn Abdul’azeez na ƙasar Saudiyya ya kira shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a waya domin yi masa ta’aziyyar rasuwar shugaban rundunar sojin ƙasa, Janar Ibrahin Attahiru tare da wasu jami’ai 10 a hatsarin jirgin sama.

Sarkin yayi jimamin wannan babban rashi da Najeriya tayi tare da miƙa ta’aziyyar sa ga shugaba Buhari a yayin da suka zanta a wayar salula ranar Litinin.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Malam Garba Shehu, shine ya bayyana haka a shafin sa na dandalin sad zumunta tuwita @GarShehu.

Garba Shehu yace: “A yau Litinin, shugaban ƙasa Buhari ya zanta da sarki Salman Ibn Abdul’azeez na ƙasar Saudiyya, lokacin da ya kira shi ya masa ta’aziyyar rasuwar shugaban sojin ƙasa, Ibrahim Attahiru, tare da wasu jami’ai 10.”

“Sarkin ya taya ‘yan Najeriya baki ɗaya jimamin wannan babban rashi na manyan sojojin da suke alfahari da su.” Hakanan kuma, shugaba Buhari da Sarki Salman sun taya juna murnar sallar Idi (Eidul Fitr) bayan kammala wata ɗaya cur ana azumin Ramadana.

Labarai Makamanta