Sarakuna Na Da Muhimmiyar Rawar Takawa Wajen Samar Da Tsaro – Monguno

Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana tasiri da muhimmancin da Sarakunan gargajiya ke dashi ta fuskar samar da tsaro a ƙasa, inda ta bayyana cewar ko shakka babu Sarakunan na da muhimmiyar rawar takawa ta fuskar tsaro muddin aka sanya su cikin tsarin.

Mai ba shugaban ƙasa shawara ta fuskar tsaro Janar Babagana Monguno ya bayyana hakan a yayin jawabin da ya gabatar wajen taron Sakatarorin Gwamnati wanda ya gudana a birnin tarayya Abuja ranar Alhamis.

Babagana Monguno, ya kuma yi kira da samun hadin kai tsakanin hukumomin tsaro dake fadin kasar nan, inda ya bukaci jihohi da su sauya salon karfafa tsarin tsaro a jihohinsu.

Mai ba da shawarar ya kara da cewa akwai bukatar saka sarakunan gargajiya wurin tattaro bayanan sirri a jihohin kasar nan, kasancewar su waɗanda suka fi kusanci da jama’a tun asali.

“Idan aka ki saka shugabannin al’umma, ba za a samu bayanan sirri da ake bukata ba,” “A halin yanzu, hukumomin tsaro basu aiki tare kamar yadda ya dace. Muna ta kokarin ganin hadin kansu.

“Ko muna so, ko bama so, Najeriya ta dogara da masarautun gargajiya. Suna da matukar muhimmanci ga tsaro kuma idan suka sauke nauyin da ke kansu, tabbas za’a samu haihuwar ɗa mai ido.

“Ba wai baiwa jama’a sarauta bane. Dole ne mu yi amfani dasu sannan suma su nuna kokarinsu.” Monguno yayi kira da sakatarorin gwamnatocin jihohi da su koma jihohinsu kuma su sasasanta da shugabanninsu domin gane amfanin sarakunan gargajiya.

Labarai Makamanta