Sanusi Ya Zama Halifan Tijjaniya A Najeriya

Tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi na II ya zama jagoran ɗariƙar Tijjaniya a Najeriya, shugaba kuma uba ga duk wani ɗan ɗariƙar Tijjaniya a tarayyar Najeriya.

An yi wannan naɗi ne a babban taron Maulidin ƙasa da ke gudana a jihar Sakkwato cibiyar Daular Uthmaniyya a tarayyar Najeriya.

Babban ɗan jagoran Tijjaniya na Afirka Khalifan Ibrahim Inyass ne ya jagoranci bikin naɗa tsohon Sarkin na Kano Muhammadu Sanusi wannan babban muƙamin.

Sanusi Lamido Sanusi ya gaji kakansa, Muhammadu Sanusi, wanda shine Khalifan Tijjaniyya na farko a Najeriya, wanda aka naɗa shi bayan sauke shi daga karagar mulki da tsohuwar Gwamnatin Arewa ta yi a shekarar 1963.

Bayan rasuwar Tsohon Sarkin ne a shekarar 1990 sai aka naɗa Sheikh Isiyaka Rabi’u a matsayin Halifan Tijjaniya a Najeriya, wanda ya jagoranci Shugabancin ta har zuwa lokacin rasuwarsa a shekarar 2018.

Tun rasuwar tsohon Khalifan Tijjaniya, Sheikh Khalifa Isyaku Rabiu a 2018, ba’a nada wanda zai maye gurbinsa ba sai yanzu. Taron ya samu halartar manyan shugabannin ɗarikar Tijjaniya a Najeriya da kasashen ketare.

Labarai Makamanta