Sanatan Kaduna: Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Uba Sani

A zaman da kotun ta yi a yau karkashin jagorancin Alkalin Kotun Mai Shari’a A.H Suleman, kotun saurarar kararrakin zabe ta Kaduna, ta tabbatar da nasarar Zababben Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya Sanata Uba Sani a matsayin halastaccen Sanata.

Hukuncin kotun ya biyo bayan karar da dan takarar Sanata na jam’iyyar PDP Adamu Lawal wanda aka fi sani da suna Mr LA ya shigar ne yana Kalubalantar nasarar Sanata Uba Sani na Jam’iyyar APC mai mulki.

A ganawar shi da manema labarai Lauya mai kare Sanata Uba Sani Barista Frank Igbe ya bayyana cewar, nasarar Sanata Uba Sani da Jam’iyyar APC a fili take, saboda sun halarci zaman kotu ne kawai domin bin doka, amma suna da tabbacin samun nasara kuma sun same ta.

Related posts