Sana’ar Fim Ta Yi Mini Komai A Rayuwa – Teema Makamashi

Fatima Isa Muhammad wadda aka fi Sani da Teemah Makamashi a harkar fim ta Masana’antar fina-finan Hausa ta Kanywood.

Ta na daya daga cikin manyan Jarumai da za a iya cewa ta wuce sahun yaran Jarumai duk da dai ba ta Kai sahun tsofaffi ba.

Ta dauki lokaci a cikin harkar don haka jaridar Dimukaradiyya ta zanta da ita Kan rayuwar ta a Masana’antar kannywwod.

Fatima Isa Muhammad ta ce “To Alhamdulillahi, Ni harkar fim babu abun da zan ce, domin na samu rufin asiri a cikin ta, don haka sai godiya ga Allah.”

Teemah Makamashi ta bayyana “Babban abun da na fi alfahari da shi a cikin harkar fim, shi ne yadda na ke zama da kowa lafiya, domin ni daman a rayuwa ta ba na son fada da kowa, to kuma sai ya zama muna zama da kowa lafiya a cikin harkar, don haka wannan abin alfahari ne a gare ni.”

A karse Teema ta yi kira ga abokan sana’ar ta da su rinka mutunta juna da Kuma rike sirrin sana’ar su.

Labarai Makamanta