Sana’ar Fim Ta Yi Mini Komai A Rayuwa – Farida Jalal


Tsohuwar Jaruma a masana’antar Finafinai ta Kannywwod, Farida Jalal wadda a shekarun baya ta yi tashen da kusan babu wata Jarumar da ta Kai ta.

Ta bayyana cewar abubuwa da dama sun faru a lokacin tana cin ganiyar ta a masana’antar wanda wasu tin tuni ta manta da su, wasu kama ba za ta taba mantawa da su ba.

Jarumar ta bayyana Hakan ne a lokacin tattaunawar su da Dimukaradiyya a Kan irin rawar da ta taka a cikin harkar fim din.

Farida Jalal ta ce “Duk da abubuwa masu yawan da su ka faru Ina cikin harkar fim, to lallai bq zan taba daina alfahari da harkar fim ba, domin ita ce sillar da duniya ta sanni, Kuma duk wani Abu da na samu ta dalilin harkar fim ne.”

Ta Kara da cewar “Babban abin da ba zan manta da shi ba a cikin harkar fim dai shi ne. Ta dalilin sa ne na yi ziyarar Masoyi na Annabi Muhammadu S A W, a lokacin ne na je aikin Hajji ni da Mahaifiya ta, na yi Umara wajen sau 4, don haka wannan abu be da ba zan taba mantawa da shi ba.

“Daga karshe ta yi Kira ga jama’ar Musulmi da su rike son Annabi da Kuma yin koyi da shi a cikin lamuran su na yau da kullum.

Labarai Makamanta